Ana Wata Ga Wata: Shugaban Amurka, Trump Ya 'Kori' Antoni Janar ana tsaka da Yakin Iran

Ana Wata Ga Wata: Shugaban Amurka, Trump Ya 'Kori' Antoni Janar ana tsaka da Yakin Iran

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami Antoni Janar ta kasa, Pam Bondi daga aiki yau Alhamis, 2 ga watan Afrilun 2026
  • Rahotanni sun nuna cewa Trump ya dauki wannan matakin ne saboda rashin gamsuwa da yadda yake gudanar da manufofinsa
  • Pam Bondi ta kasance mace mai biyayya da nuna goyon baya ga Shugaba Trump tun shekarar 2016, kuma tana cikin lauyoyin da suka tsaya masa a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa Antoni Janar, Pam Bondi, za ta bar mukaminta a yau Alhamis, 2 ga watan Afrilu, 2026.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa shugaban kasar ya nuna damuwa kan yadda take gudanar da wasu muhimman kudurorinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu, Obi ko Atiku? Malaman addini sun yi hasashen wanda zai lashe zaben 2027

Shugaban Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trumo a fadar White House Hoto: Samuel Corum
Source: Getty Images

Trump ya sallami Antoni Janar ta Amurka

A wani sako da ya wallafa a dandalin Truth Social, Trump ya bayyana cewa:

"Muna kaunar Pam, amma a yanzu za ta bar mukaminta, za ta koma wani sabon aiki a bangaren kamfanoni masu zaman kansu nan ba da dadewa ba."

Shugaban ya kuma sanar da cewa mataimakin Antoni Janar, Todd Blanche, shi ne zai karbi ragamar ma'aikatar a matsayin mai rikon kwarya.

Duk da kalaman yabo na fili, wasu majiyoyi daga fadar White House sun shaida wa kafar yada labarai ta NBC News cewa a zahiri kora aka yi wa Bondi.

Majiyar ta ce Trump ya dade yana nuna damuwa kan yadda Bondi ba ta aiwatar da "burinsa" yadda yake so ba, duk da cewa yana kaunarta a matsayin mutum.

Tarihin Bondi da alakarta da Trump

Pam Bondi ta kasance mace mai biyayya ga Trump tun shekarar 2016, inda aka taba jinta tana goyon bayan kiran "a garkame ta" da aka yi wa Hillary Clinton.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: Trump ya jefawa mataimakinsa zargi kan yakin Iran

Ta kasance daya daga cikin lauyoyin da suka kare shi lokacin da aka nemi tsige shi daga mulki a karon farko, sannan ta yi ikirarin cewa ya lashe zaben 2020 a jihar Pennsylvania duk da cewa ya sha kaye.

A lokacin da take kan mulki, Bondi ta jagoranci korar daruruwan lauyoyi da jami'an FBI wadanda ke da alaka da binciken ayyukan Trump.

Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump da tsohuwar Antoni Janar, Pam Bondi Hoto: Saul Loeb
Source: Getty Images

Wanene Todd Blanche?

Todd Blanche, wanda tsohon lauyan Donald Trump ne na kashin kansa, ya gode wa shugaban bisa wannan amana da ya dora masa.

Blanche ya kasance jagoran lauyoyin da suka kare Trump a shari'ar da aka yi masa kan zargin karya dokar adana bayanan kasuwanci da biyan kudin rufa-baki ga jarumar fina-finai, Stormy Daniels.

Trump ya yi barazanar fita daga NATO

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa kasashen Turai barazana game da kungiyar tsaro ta NATO da suka kafa tun a shekarar 1949.

Donald Trump ya shaida cewa yana matuƙar tunanin fitar da Amurka daga ƙungiyar NATO bayan ta kasa shiga yaƙin da yake yi da Iran.

Shugaban ya bayyana ƙungiyar a matsayin mai rauni, yana mai cewa cire Amurka daga yarjejeniyar tsaro yanzu ya wuce batun sake tunani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262