Ba Sauki: Amurka da Isra'ila Sun ga Ta Kansu, Iran Ta Kaddamar da Zazzafan Hari

Ba Sauki: Amurka da Isra'ila Sun ga Ta Kansu, Iran Ta Kaddamar da Zazzafan Hari

  • Rundunar IRGC ta kasar Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan Amurka da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya
  • IRGC ta kaddamar da rukuni na 90 na hare-haren ramuwar gayya da take kai wa tun bayan fara yaki a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026
  • Rundunar IRGC ta bayyana hare-haren na ta sun lalata wurare masu muhimmanci na Amurka da Isra'ila tare da hallaka sojoji

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ƙaddamar da rukuni na 90 na harin ramuwar gayya mai suna 'Operation True Promise 4'

Rundunar IRGC ta farmaki masana’antun Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da masana’antun ƙarfe da na dalma a ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Bahrain.

Iran ta kaddamar da hare-hare kan Amurka da Isra'ila
Makami mai linzami na Iran da aka harba Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce rundunar IRGC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 2 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Yaki ya rincabe: Iran ta harba makamai 300 lokaci 1 kan sojojin Amurka da Isra'ila

Rundunar IRGC ta ce waɗannan hare-hare ramuwar gayya ce kan hare-haren da aka kai wa masana’antun Iran a baya, sannan ta yi gargaɗin ƙara tsananta yakin idan aka ci gaba da kai mata hari.

Barnar da hare-haren Iran suka yi

Ofishin hulɗa da jama'a na IRGC ya tabbatar da cewa wani haɗaɗɗen samamen makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa ya yi nasarar lalata muhimman ababen more rayuwa da ke da alaƙa da sojojin Amurka da Isra'ila a yankin.

Sanarwar ta IRGC ta ba da bayani dalla-dalla kan lalata masana'antun ƙarfe masu alaƙa da Amurka da ke Abu Dhabi (UAE), da kuma masana'antun dalma masu alaƙa da Amurka a Bahrain, waɗanda aka ce sun tsira daga hare-haren baya.

Haka zalika, samamen ya shafi wuraren adana makaman sojojin Amurka, ciki har da masana'antun kera makamai na Rafael da kuma wasu ɓoyayyun sansanonin dakarun Amurka da ke kusa da Manama, babban birnin Bahrain.

IRGC ta ce ta kashe sojojin Amurka

Haka kuma, IRGC ta bayar da rahoton cewa an kashe tare da jikkata da dama daga cikin jami'an Amurka yayin harin, kuma jami'an tsaro sun killace yankin nan take, rahoton Palestine Chronicle ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta bar boye boye, ta bayyana adadin waɗanda suka jikkata a yaki da Iran

Ta ce an shafe sa'o'i ana jigilar motocin asibiti yayin da ake kwashe jami'an da suka ji rauni.

A cikin sanarwa kan mataki na biyu na rukuni na 90, ofishin hulɗa da jama'a na IRGC ya bayyana cewa sun kuma kai hari kan sansanonin sojojin sama na Isra'ila a Tel Nof, Palmachim, da Ben Gurion, tare da wuraren taron sojoji a Tel Aviv, Haifa, Eilat, Negev, da Beersheba.

Sansanonin sojin Amurka na Ahmad al-Jaber da Ali al-Salem a Kuwait, da kuma al-Kharj a Saudiyya, su ma sun fuskanci harin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

IRGC ta bayyana waɗannan hare-hare a matsayin ɓangare na babban tsarin ramuwar gayya ga "ayyukan laifuka" da Amurka da Isra'ila suka aikata, ciki har da hare-haren da aka kai wa biranen Iran da masana'antunta.

Iran ta kai hare-hare kan Amurka da Isra'ila
Makami mai linzami na Iran da aka harba daga jikin mota Hoto: @IRIran_Military
Source: Twitter

Iran ta gargadi Donald Trump

Sanarwar ta kuma fitar da gargaɗi kai-tsaye ga Shugaban Amurka Donald Trump, inda ta ba shi shawarar ya guji ƙarin wasu ayyuka da za su iya faɗaɗa wannan yaƙin ta'addanci kan Iran zuwa wajen yankin, wanda hakan zai sa duniya ta ƙara zama haɗari ga Amurka.

Kara karanta wannan

Yaƙi ya ɗauki zafi: Iran ta lissafa manyan kamfanonin Amurka 18 da za ta farmaka

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"An sadaukar da wannan samamen ne ga iyalan ma'aikatan da suka yi shahada a hare-haren baya."

Iran ta harba makamai kan Amurka, Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta kasar Iran ta kaddamar da hare-hare kan Isra'ila da Amurka.

Rundunar IRGC ta bayyana cewa ta ta yi ruwan wuta kan wurare daban-daban na sojin Amurka da Isra'ila a faɗin yankin Tekun Fasha.

A gagarumin harin, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar dakarun "resistance fronts," an yi amfani da makamai masu linzami sama da 100, jirage marasa matuƙa, da kuma wasu rokoki 200.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng