Bayan Haura Wata 1 Ana Yaki, Shugaba Macron Ya Fada Wa Amurka Gaskiya kan Shirin Nukiliyar Iran

Bayan Haura Wata 1 Ana Yaki, Shugaba Macron Ya Fada Wa Amurka Gaskiya kan Shirin Nukiliyar Iran

  • Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce karfin soji ba zai iya rusa shirin nukiliyar Iran ko bude mashigar ruwa ta Hormuz ba
  • Macron ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi kan rikicin Gabas ta Tsakiya a wata ziyara da ya kai kasar Koriya Ta Kudu
  • Ya bukaci Amurka da Isra'ila su janye daga kai hare-hare Iran, su koma teburin tattaunawar diflomasiyya domin warware komai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

France - Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana hasashensa kan yunkurin da Amurka ke yawan ikirarin tana yi don lalata duk wani shirin nukiliyar kasar Iran.

Bayanai sun tabbatar da cewa kasar Faransa dai na daya daga cikin kasashen duniya da ke da alaka ta kusa da Amurka.

Macron.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron a wurin taron kasa da kasa Hoto: Franck Robichon
Source: Getty Images

Faransa ta fadawa Amurka/Isra'ila gaskiya

Sai dai duk da dasawar da kasashen biyu ke yi, Shugaba Macron ya fito ya bayyana cewa ba za a iya rusa shirin nukiliyar Iran ta hanyar yaki ba, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

A jawabin da ya yi, shugaban kasar na Faransa, Emmanuel Macron, ya yi tsokaci kan sababbin al'amuran da ke faruwa a kasar Iran da kuma rikicin mashigar ruwa ta Hormuz

Macron ya yi wannan magana ne yayin wata ziyara ta musamman da ya kai kasar Koriya ta Kudu a daidai lokacin da ake muaayar wuta tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila.

Ya bayyana cewa hare-haren da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kan Iran ba za su taba magance matsalar shirin nukiliyar kasar ba, in ji rahoton Vanguard.

Shugaban Faransa ya kawo mafita

Ya bai wa kasashen biyu shawarar cewa maimakon daukar matakin soji, kamata ya yi su dawo su bi hanyar diflomasiyya domin sasanta lamarin cikin ruwan sanyi.

“Idan babu tsarin tattaunawa na diflomasiyya da fasaha, lamarin zai iya sake dagulewa nan da 'yan watanni ko 'yan shekaru,” in ji Macron.

Haka zalika, shugaban na Faransa ya yi watsi da shawarar kai samamen soja domin bude mashigar ruwa ta Hormuz, inda ya bayyana shirin a matsayin “marar amfani” ko kuma abin da ba zai yiwu ba.

Trump da Macron.
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron Hoto: Ludovic Marin
Source: Getty Images

Macron ya roki a bi Iran ta lalama

Kara karanta wannan

A karshe, Trump zai hakura da yakin Iran ko ba yarjejeniya, ya saka lokaci

A kwanakin baya dai Shugaba Donald Trump na Amurka ya nemi kasashen Turai ciki har da Faransa da su taimaka wa Amurka wajen bude mashigar ruwan Hormuz da karfi da yaji.

Macron ya kara da cewa:

“Zai dauki lokaci mai tsawo sosai, sannan zai jefa duk wanda ya ratsa mashigar cikin barazanar hare-hare daga dakarun kare juyin juya halin Musulunci (RGC), wadanda ke da tarin makamai, da makamai masu linzami da sauran abubuwa masu hatsari."

Iran ta kakkabo jirgin Amurka/Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake yi wa Amurka/Isra'ila barna yayin da kasashen ke ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu.

Rundunar sojin Iran ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin yaki marar matuki kirar MQ-9 a kusa da birnin Isfahan, wanda ta ce abokan gabarta, Amurka da Isra'ila ne.

Jirgin MQ-9 Reaper na daga cikin manyan jiragen leken asiri da ake amfani da su wajen kai hare-hare da tattara bayanai, kuma darajarsa na kai kusan Dala miliyan 30

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262