Hukuncin Kisa: Kasashen Musulmi 8 Sun Dauki Zafi, Sun Maida Martani ga Isra'ila

Hukuncin Kisa: Kasashen Musulmi 8 Sun Dauki Zafi, Sun Maida Martani ga Isra'ila

  • Dokar da Majalisar Isra'ila ta amince da ita ta hukuncin kisa kan Falasdinawa na ci gaba da jan hankalin kasashen duniya
  • Kasashe takwas da al'ummar musulmi suka fi rinjaye sun caccaki Isra'ila kan wannan doka wacce suka ce ta nuna wariya da tauye hakkin dan adam
  • Sun bayyana cewa dokar ta nuna kiyayya karara ga al'ummar Falasdinawa, wadanda aka tabbatar da suna fuskantar azabtarwa a hannun Isra'ila

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Middle East - A farkon wannan mako, majalisar dokokin Isra’ila ta amince da wani ƙudirin doka mai fuska biyu, wanda ya kunshi hukuncin kisa ga Falasdinawa da rangwame ga Yahudawa.

Dokar ta umarci kotunan sojin Isra'ila da su yanke hukuncin kisa ga Falasɗinawa idan aka same su da laifin kashe ’yan Isra’ila a matsayin laifuffukan "ta’addanci."

Kara karanta wannan

Yahudawa sun ga ta kansu da makamin Iran ya afka masu a babban birnin Isra'ila

Firaministan Isra'ila.
Firaministan kasar Isra'ila da Yahudawa suka mamaye, Benjamin Netanyahu Hoto: Ronen Zvulun
Source: Getty Images

A rahoton tashar Al-Jazeera, Majalisar ta ce dokar ba za ta yi aiki a kan Yahudawa ’yan Isra’ila da aka samu da laifin kashe Falasɗinawa ba, lamarin da ya jawo hankulan kasashen duniya.

Kasashen musulmi 8 sun yi tir da dokar

Bisa haka ne kasashe takwas da musulmi suka fi rinjaye suka yi zama tare da daukar matsaya kan wannan doka ta Isra'ila, wacce ake ganin babu adalci kwata-kwata a cikinta.

Kasashenn da suka kunshi Pakistan, Turkiyya, Masar, Indonesia, Jordan, Qatar, Saudi Arabia, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi Allah-wadai da wannan doka.

Ministocin harkokin waje na wadannan ƙasashe takwas da Musulmi suka fi rinjaye ne suka rattaba hannu a wannan sanarwa

Ministocin sun yi gargaɗi game da "irin wadannan ayyuka na Isra’ila masu cike da nuna wariya da kuma tsananta lamura, waɗanda ke ƙarfafa tsarin wariyar launin fata."

Kara karanta wannan

Yaki ya rincabe: Iran ta harba makamai 300 lokaci 1 kan sojojin Amurka da Isra'ila

"Wannan ra’ayi ne na ƙiyayya da ke tauye haƙƙoƙin da ba za a iya danne wa wata al'umma ba, kuma bazara ce ga wanzuwar al’ummar Falasɗinu a yankunansu da aka mamaye," in ji sanarwar.

An tono azabar da ake wa Falasdinawa

Haka kuma, sun nuna "damuwa mai radadi" game da yanayi da halin da fursunoni Falasɗinawa ke ciki a gidan yarin Isra’ila, kamar yadda DW ta ruwaito.

Kasashen sun yi nuni da "rahotanni ababen dogaro" daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam game da azabtarwa, yunwa, da kuma "tauye haƙƙoƙin yau da kullum," da ake wa Falasdinawa a gidajen yarin Isra'ila.

Falasdinawa.
Wasu daga cikin Falasdinawa suna kokarin komawa gida bayan tsagaita wuta a Gaza Hoto: Jaafar Ashtiyeh
Source: Getty Images

Tuni dai ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da wasu daidaikun ƙasashen Turai suka fito fili suka soki wannan sabuwar doka da Isra'ila ta bullo da ita.

Iran ta jikkata yahudawa a Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa kukumomin kasar Yahudawa watau Isra'ila sun bayyana wasu daga cikin barnar da hare-haren Iran suka yi wa mutane a kusa da Tel Aviv.

Hukumomin da ke da alhakin kai dauki da ba da agajin gaggawa na Isra'ila ce makamin da Iran ta harbo ya raunata mutane 14 a yankin Bnei Brak.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Magen David Adom ta bayyana cewa ta duba mutane 14 da suka raunata a yankin Bnei Brak tare da kwashe su zuwa asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262