Trump: Amurka Ta Tsara Shiga Iran da Dubban Sojoji da Kayan Tono Sinadarai

Trump: Amurka Ta Tsara Shiga Iran da Dubban Sojoji da Kayan Tono Sinadarai

  • Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin Amurka sun gabatarwa shugaba Donald Trump wani shiri na musamman da suka tsara kan shiga Iran
  • Shirin zai bukaci tura dubban sojojin kasa da kayan aiki domin tono sinadaran uranium da Iran ta ajiye a wani waje da ake cewa na nukiliya ne
  • Wasu jami'an Amurka sun bayyana cewa shirin yana da hadari sosai, kuma zai bukaci dogon lokaci kafin a iya aiwatar da shi cikin nasara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Rahotanni sun ce sojojin Amurka sun gabatar wa shugaban ƙasa Donald Trump wani shiri mai matuƙar wahala na aiki na musamman domin fitar da kimanin kilo 453.6 na sinadarin uranium da aka birne a ƙasar Iran.

A cewar rahotanni, Trump ne ya buƙaci a gabatar masa da wannan shiri, lamarin da ke nuna yana da niyyar kawar da ƙarfin nukiliyar Iran gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

A karshe, Trump zai hakura da yakin Iran ko ba yarjejeniya, ya saka lokaci

Shugaba Donald Trump da sojojin Amurka
Donald Trump na yi wa sojojin Amurka jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da jaridar Washington Post ta wallafa ya nuna cewa wasu jami'an kasar Amurka sun sanar da cewa shirin yana da hadarin gaske.

Shirin kasar Amurka na shiga Iran

Wasu tsofaffin jami’an tsaro sun bayyana cewa shirin aikin zai buƙaci jigilar dubban sojoji da manyan kayan tono zuwa Iran ta jirgin sama, kuma zai iya ɗaukar makonni kafin a kammala shi.

Bisa bayanan da aka samu, an ce dole ne sojojin su fara kai hari Iran ta sama sannan su kafa sansani, mai yiyuwa ta hanyar saukar da jirage na rundunar soji domin mamaye yankin da kuma gina filin saukar jirage domin kai kayan aiki.

Bayanin wani tsohon sojan Amurka

Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa wani tsohon jami’in soja ya bayyana aikin a matsayin abin da zai dauki lokaci kafin aiwatar da shi.

“Dole zai tafi a hankali, yana buƙatar kulawa sosai kuma yana da haɗarin gaske.”

Kara karanta wannan

Pakistan ta faɗi halin da ake ciki a kokarin sulhunta Iran da Amurka

Abin da Amurka ke son kaiwa farmaki shi ne wajen ajiyar sinadarin uranium na Iran da aka tace kuma ya kai kashi 60 cikin 100, wanda bai kai matakin kera makamin nukiliya ba.

An ce mafi yawan wannan sinadari yana ƙarƙashin wuraren nukiliya da aka kai wa hari a wani farmakin Amurka da aka yi a watan Yunin 2025.

Shugaban Amurka a wajen wani taro
Shugaba Donald Trump na yi wa wasu 'yan Amurka bayani. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Martanin kasar Iran ga Amurka

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da cewa sinadarin yana ƙarƙashin wasu gine-gine kuma babu shirin gaggawa da zai yi nasarar kwato shi.

Lokacin da aka tambayi Shugaba Donald Trump ko kwato uranium ɗin sharadi ne na ayyana nasara a yaƙin, bai bayar da amsa kai tsaye ba.

Trump zai raba hanya da NATO

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar fita daga kungiyar NATO saboda sabanin da suka samu a yakin Iran.

Trump ya bayyana haka ne yayin hira da menema labarai, inda ya ce kasashen NATO sun gagara shiga fadan da Amurka ta fara da Tehran.

Shugaban Amurka ya nuna cewa kasar shi ta kasance tana gaba-gaba wajen tallafawa NATO amma abin mamaki kungiyar ta juya masa baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng