Da Alama Yaki Ya Zo Karshe, Kasar Musulunci Ta Iran Ta Karbi Sako daga Amurka
- A karshe dai Iran ta tabbatar da cewa ta karbi sakon bukatar tsagaita wuta a yanin da kasar ta shafe sama da wata guda tana yi da Amurka da Isra'ila
- Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta tabbatar da karbar sakon ta hannun masu shiga tsakani, ta ace ta fara nazari kan abubuwan da ta gani
- Tun farko dai Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya musanta rade-radin cewa sun hau teburin tattaunawa da Amurka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin kasar Musulunci ta Iran ta gabbatar da cewa ta karbi sakon neman tsagaita wuta a yakin da take yi da kasashen Amurka da Isra'ila.
Iran ta bayyana cewa ta samu wannan sako na neman kawo karshen wannan yaki da ya shafe sama da wata daya ana barin wuta a Gabas ta Tsakiya, ta hannun masu shiga tsakani.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Shugaban Iran ya aika budaddiyar wasika zuwa Amurka ana tsaka da yaki

Source: Getty Images
Rahoton da tashar Al-Jazeera ta kawo ya nuna cewa duk da haka, Iran ta sake jaddada cewa hakan ba yana nufin ta hau teburin tattaunawar diplomasiyya da Amurka ko Isra'ila ba ne.
Iran ta samu sakon neman tsagaita wuta
Kakakin Ma’aikatar Wajen ƙasar Iran, Esmaeil Baghaei, ne ya bayyana hakan, yana mai tabbatar da cewa masu shiga tsakani sun mika wa kasar bukatun tsagaita wuta.
Ya bayyana cewa Tehran ta karɓi wasu saƙonni ta hannun waɗanda ke shiga tsakani, kuma a halin yanzu ana nazari a kan waɗannan saƙonni.
"Abin da yake da mahimmanci ga al’ummar Iran shi ne kare kansu daga wannan zalunci, kuma a shirye muke don fuskantar kowane irin hari, har ma da harin sojojin ƙasa,” in ji shi.
Iran ta sha musanta tattaunawa da Amurka
Idan baku manta ba a farkon wannan makon ne babban jami’in diflomasiyyar Iran watau ministan harkokin waje, Abbas Araghchi, ya ce babu wata tatataunawa da suka fara da Amurka.
Ya kara da cewa ko da yake Iran ta karɓi saƙonni daga wakilin Amurka na musamman, Steve Witkoff, "wannan ba yana nufin cewa muna cikin tattaunawa ba ne."
Bayan haka kuma, shugaban Amurka, Donald Trump ya fito ya yi ikirarin cewa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya nemi a tsagaita wuta a yakin, wanda ya haura wata guda ana yi.

Source: Getty Images
Da yiwuwar a tsagaita wuta a yakin Iran
Sai dai cikin sa'o'i kadan ma'aikatar wajen Iran ta fito ta karyata wannan ikiirari na Trump, inda ta bayyana shi a matsayin karya mara tushe ballantana makama.
Amma a daren ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2026, kakakin ma'aikatar, Esmaeil Baghaei ya tabbatar da cewa Iran ta samu sako kan batun tsagaita wuta ta hannun masu shiga tsakani, in ji rahoton NBC News.
Shugaban Iran ya tura sako ga Amurkawa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya rubuta wata buɗaɗɗiyar wasika ta musamman zuwa ga al’ummar kasar Amurka.
Shugaba Pezeshkian ya yi fatali da yadda ake nuna Iran a matsayin barazana ga tsaro, yana mai cewa hakan bai yi daidai da gaskiyar tarihi ba.
Pezeshkian ya tuna kyakkyawar alakar da ke tsakanin Amurka da Iran a baya tare da jero abubuwan da suka rusa wannan dangantaka.
Asali: Legit.ng
