Babbar Magana: Shugaban Iran Ya Aika Budaddiyar Wasika zuwa Amurka ana tsaka da Yaki

Babbar Magana: Shugaban Iran Ya Aika Budaddiyar Wasika zuwa Amurka ana tsaka da Yaki

  • Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya yi bayani kan kashin kajin da ake shafawa kasarsa a wata budaddiyar wasika da ya aika wa Amurkawa
  • Ya yi bayani kan zargin da ake cewa Iran ta zama barazana ga tsaron wasu kasashe, inda ya ce kasar ba ta taba haddasa yaki ba a tarihi
  • Shugaba Pezeshkian ya tuna kyakkyawar alakar da ke tsakanin Amurka da Iran a baya tare da jero abubuwan da suka rusa wannan dangantaka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya rubuta wata buɗaɗɗiyar wasika da ya yi mawa take na musamman zuwa ga al’ummar kasar Amurka.

Shugaba Pezeshkian ya yi fatali da yadda ake nuna Iran a matsayin barazana ga tsaro, yana mai cewa hakan "bai yi daidai da gaskiyar tarihi ba."

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

Shugaban Iran.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian a wurin taro Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Shugaban Iran ta dauko tsohon tarihi

A rahoton da tashar Al-Jazeera ta tattaro, shugaban ya jaddada cewa a tarihin Iran na tsawon zamani, ba ta taɓa zaɓar hanyar ta’addanci, mamaya, mulkin mallaka, ko danniya ba.

"Iran, ta fuskar sunanta, halayyarta, da asalinta, tana ɗaya daga cikin tsofaffin kasashe masu wayewa a tarihin ɗan adam. Iran ba ta taɓa tada yaƙi ba amma duk da haka, a shiryetake wajen kare kanta daga duk wanda ya kawo mata hari.
"Nuna Iran a matsayin haɗari (ga tsaro da zaman lafiya) ba komai ba ne face wani shiri na son rai da kuma biyan buƙatun wasu daban," in ji Pezeshkian.

Ya bayyana cewa siffanta Iran a matsayin barazana "ba gaskiya ba ne," face dai wani shiri ne na masu iko don halasta matsin lamba, riƙe iko, bunkasa masana'antun makamai, da mallakar kasuwannin duniya.

Dalilan Iran na kin yarda da Amurka

Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa rashin yardar da ƙasarsa ke yi wa Washington a halin yanzu ta samo asali ne daga dalilai da dama, ciki har da yi mata katsalandan da kuma "takunkumi na rashin tausayi."

Kara karanta wannan

Rundunar IRGC ta yi wa Isra'ila barna a sababbin hare haren makami mai linzami

Ya bayyana cewa a baya babu wata matsala ko gaba da juna a dangantakar Iran da Amurka, kuma mu'amala tsakanin al'ummar ƙasashen biyu tana da kyau a wancan lokaci.

Shugaba Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Abubuwan da suka lalata alakar Amurka da Iran

Sai dai, ya nuna cewa juyin mulkin 1953, shi ne "ya sauya komai" inda ya bayyana shi a matsayi haramtacciyar hanyar da Amurka ta bi don hana Iran mallakar arziƙin man fetur ɗinta, cewar New York Post

Haka zalika ya ambaci goyon bayan da Amurka ta ba wa shugaban Iraki Saddam Hussein lokacin yaƙin Iran da Iraki da takunkumi mai tsanani da hare-hare a matsayin abubuwan da suka ruguza alakar kasashen biyu

A ƙarshe, Shugaban na Iran ya bayyana cewa ci gaba da kai hare-haren soja da bama-bamai na baya-bayan nan yana matuƙar shafar rayuwar mutane, tunaninsu, da kuma mahangarsu game da Amurka.

Iran ta yi fatali da kalaman Shugaba Trump

A baya, kun ji cewa gwamnatin Iran ta musanta ikirarin da Shugaba Donald Trump ya yi cewa shugaba Masoud Pezeshkian ya nemi a tsagaita wuta a yakin da ke gudana.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara maganar laftawa Larabawa kudin diyya kan yakin Trump da Iran

Trump dai ya bayyana cewa shugaban kasar Iran ya tuntube shi yana neman a tsagaita wuta a yakin wanda aka kwashe fiye da wata daya ana gwabzawa.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya yi watsi da kalaman Shugaban Amurka ta tsagaita wuta, inda ya bayyana hakan a matsayin ƙarya mara tushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262