Matsin Lambar Amurka Ya Tilasta wa Birtaniya Faɗin Matsayarta kan Yakin Iran da Isra'ila

Matsin Lambar Amurka Ya Tilasta wa Birtaniya Faɗin Matsayarta kan Yakin Iran da Isra'ila

  • Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya bayyana matsayar kasar kan yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Stermer ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta shiga rikicin Iran ba, yana mai cewa wannan yaƙi ba nasu ba ne
  • Starmer ya jaddada cewa gwamnati za ta kare rayukan ‘yan Birtaniya da muradunsu a yankin, tare da goyon bayan kawaye amma ba shiga kai tsaye ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

London, UK - Kasar Birtaniya ta bayyana matsayarta kan ci gaba da yaki da ake yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Isra'ila.

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya bayyana cewa ƙasar Birtaniya ba za ta shiga rikicin da ke gudana da Iran ba.

Birtaniya ta tabbatar da cewa ba za ta shiga yakin Iran da Amurka
Firayim ministan Birtaniya, Keir Stermer da Shugaba Donald Trump. Hoto: @Keir_Stermer, Donald J Trump.
Source: Twitter

Matsayar Birtaniya kan yakin Iran da Isra'ila

Stermer ya bayyana haka ne yayin martani kan yakin yana mai jaddada cewa wannan lamari ba yaƙin su ba ne, cewar Anadolu Ajansi.

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

Rahotanni sun nuna cewa Starmer ya ce matsayar gwamnatinsa a bayyane take duk da karuwar tashin hankali a yankin, yana mai cewa ba za a ja su cikin rikicin ba.

Ya ce yana da muhimmanci ya sake fayyace matsayinsa da na gwamnati, yana mai cewa wannan ba yaƙinsu ba ne kuma ba za su bari a ja su ciki ba.

Firaministan ya kara da cewa duk da haka Birtaniya za ta dauki matakan kare ‘yan kasarta da muradunta na dabaru a yankin, tare da tsayawa tare da kawayenta.

Ya ce za su kare rayukan ‘yan kasar Birtaniya da muradunsu a yankin, kuma za su goyi bayan kawayensu a yankin Tekun Gulf ba tare da shiga kai tsaye ba.

Trump na ci gaba da matsawa kasashe kan yaki da Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Dalilin kin shigan Birtaniya yakin Isra'ila/Iran

Starmer ya jaddada cewa matsayinsa ya samo asali ne daga ƙa’idoji, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da bin wannan hanya duk da matsin lamba.

Ya ce ba za su bari a ja su cikin rikicin ba, yana mai cewa wannan ne tushen kimarsu da kuma yadda suka yanke shawara duk da matsin lamba, cewar rahoton TRT World.

Kara karanta wannan

A karshe, Trump zai hakura da yakin Iran ko ba yarjejeniya, ya saka lokaci

Kalaman nasa sun zo ne a lokacin da ake ci gaba da damuwa a duniya game da yiwuwar rikicin ya kara faɗaɗa a yankin da kuma haifar da sabon tashin hankali.

Sai dai kasashe da dama sun bayyana cewa ba za su shiga fadan ba duk da yadda Amurka ke nuna damuwa kan rashin ba da gudunmawarsu.

Yakin Iran/Isra'ila: Birtaniya ta ba Amurka gudunmawa

Mun ba ku labarin cewa salon yaki na shirin sauyawa a Gabas ta Tsakiya yayin da aka shafe kwanaki ana gwabzawa tsakanin Iran da kasashen Amurka da Isra'ila.

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ba Amurka damar amfani da sansanin sojinsu wajen kare kai daga hare-haren Iran a wata sanarwa da ya fitar.

A kwanakin baya, shugaban Amurka, Donald Trump ya nemi a ba shi damar amfani da sansanin amma Birtaniya ta ce hakan ba zai yiwu ba sam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.