Amurka da Isra'ila Sun Shiga Uku, Mojtaba Khamenei Ya Aika Wasika ga Shugaban Hezbollah
- Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ya jaddada goyon bayan kasarsa ga kungiyar Hezbollah yayin da suke ci gaba da yaki da Amurka da Isra'ila
- Ya gode wa shugaban Hezbollah, Naim Qassem, bisa sakon ta’aziyyar da ya aika masa bayan rasuwar mahaifinsa, Ali Khamenei
- Hukumomin Iran sun musanta harba makami mai linzami zuwa kasar Turkiyya, inda suka cewa labarin kanzon kurege ne
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tehran – Jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei ya aika wata wasika ta musamman ga shugaban kungiyar Hezbollah, Naim Qassem.
Khamenei ya yi alkawarin ci gaba da maida martani a yakin Iran da Amurka da Isra’ila a cikin wannan sako da ya aikawa shugaban Hezbollah.

Source: Twitter
A rahoton The Times of India, jagoran ya kuma nuna godiya bisa ta’aziyyar da aka yi masa bayan rasuwar mahaifinsa, tsohon jagoran addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Khamenei ya tura sako ga Shugaban Hezbollah
A cikin wasiƙar, Khamenei ya gode wa Qassem kan ta’aziyya da ya aika masa bayan “shahadar” Ali Khamenei a harin jiragen sama da Amurka da Isra’ila suka kai Teharan a ranar farko ta yakin.
Ya bayyana jin dadinsa bisa “kauna da biyayya” da mayakan Hezbollah suka nuna wa Iran, yana mai cewa wannan abu da suka yi na shiga yakin ya nuna jajircewar da suke da ita.
Khamenei ya ce dagewa da juriya a gaban “maƙiyan da ba su kaunar al’ummar Musulmi, wato Amurka da Yahudawa” na daga cikin halayen marigayi mahaifinsa.
Iran ta jaddada goyon bayan Hezbollah
Ya kuma shaida wa Qassem cewa yana jagorantar kungiyar Hezbollah a “lokaci mai muhimmanci,” yana mai nuna tabbacin cewa hikimarsa, basira da jarumtarsa za su karya lagon Yahudawa tare da dawo martabar kasar Lebanon.
Wannan sako, wanda kafofin labarai da dama ciki har da tashar Al-Jazeera suka ruwaito, ya sake tabbatar da goyon bayan Tehran ga kungiyoyi irinsu Hezbolla a daidai lokacin da yaki da Amurka/Isra'ila ke kara zafi.
Khamenei, wanda Majalisar Iran ta nada a matsayin jagora a ranar 8 ga Maris 2026, ya yaba da jagoranci da jarumta da sadaukarwar mayakan Hezbollah, yana mai kara tabbatar da haɗin tsakanin Iran da kungiyar.

Source: Getty Images
Iran ta musanta kai hari Turkiyya
A karshe, jagoran Iran ya jaddada cewa kasar za ta ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya da kare kai kan makiyanta, Amurka da Isra'ila, ba tare da gajiya ko ja da baya ba.
Bugu da kari, Gwamnatin Iran ta karyata rahotannin da ke cewa dakarun sojojinta sun harba makami mai linzami zuwa Turkiyya, inda ta bayyana rahoton a matsayin "mara tushe.”
Iran ta yi barazanar kai hari kamfanoni
An ji cewa Rundunar IRGC ta Iran ta lissafa manyan kamfanonin Amurka guda 18 wadanda za ta kai wa hari daga daren ranar Laraba, 1 ga Afrilun 2026.
Wadannan kamfanoni da Iran za ta farmaka sun hada da Boeing, Tesla, Meta, HP, Microsoft, Google, da Apple, wadanda dukansu mallakin 'yan kasar Amurka ne.
Rundunar ta IRGC ta buƙaci dukkan ma'aikata da mutanen dake zaune kusa da ofisoshin waɗannan kamfanoni da su fice cikin gaggawa kafin lokacin da aka ɗiba na fara kai hare-haren.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

