Mamaki Ya Kama Isra'ila da Makaman Iran Suka Lalata Dakunan Kariyarta

Mamaki Ya Kama Isra'ila da Makaman Iran Suka Lalata Dakunan Kariyarta

  • Harin makamai masu linzami daga Iran ya kashe mutane biyar a tashin farko bayan an saita tsakiyar Isra’ila
  • Sai dai rahotanni sun bayyana cewa an samu karuwar adadin mutanen da suka kwanta dama yayin harin ramuwar
  • Haka kuma gidaje da dama sun lalace a Petah Tikva da Bnei Brak bayan fashewar wani makami da ya dura a yankunan da daddare

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Israel – Wani mummunan hari na makamai masu linzami da Iran ta kai cikin dare ya afkawa tsakiyar Isra’ila a safiyar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026 ya kashe mutane da yawa.

A tashin farko da makaman suka sauka, harin ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Amurka ta ci karo da cikas, Iran ta illata ta a yakinta da kasar Isra'ila

Isra'ila ta ji ba dadi a wani harin Iran
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sanye da rigar kariya ta yaki Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Facebook

Aljazeera ta wallafa cewa amma an samu karuwar mutanen da suka rasu, wanda aka tabbatar yanzu mutum 14 sun koma ga Ubangijinsu.

Harin Iran ya girgiza Isra'ila

Times of Israel ta ruwaito cewa harin ya girgiza al’umma musamman a biranen Petah Tikva da Bnei Brak.

Jama'a sun farka da jin karar fashe-fashe, rushewar gine-gine da kuma tsoron yakin da ya zo kofar gidajensu.

A Petah Tikva, wani makami mai linzami ya bugi wani ginin bene mai hawa da dama kai tsaye, inda ya kashe mutane hudu tare da lalata wasu gine-gine da ke kusa.

Ana bincike a kan wani harin Iran a Isra'ila
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana bayani Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Getty Images

Fashewar ta yi karfi matuka, inda ta fasa tagogi, ta lalata makaranta da ke kusa, sannan ta tarwatsa gilashin motoci a yankin.

Mazauna yankin sun shafe sa’o’i a waje suna jira, wasu dauke da kananan jakunkuna, kafin jami’an tsaro su ba su damar komawa cikin gidajensu domin daukar muhimman kayayyaki.

Kara karanta wannan

Rundunar IRGC ta yi wa Isra'ila barna a sababbin hare haren makami mai linzami

Makaman kariyar Isra'ila sun gaza

A cewar rundunar sojin Isra’ila, makamin ya samu nasarar kutsa cikin wani dakin kariya da aka kera domin jure irin wadannan hare-hare.

Sai dai rundunar ta ce wannan al'amari ne da ba kasafai ake gani ba. Jami’an tsaro sun bayyana cewa wannan lamari na musamman ne, inda makami ya bugi dakin kariya kai tsaye.

Sun kara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano yadda hakan ta faru. Duk da haka, sun jaddada cewa dakunan kariya har yanzu su ne mafi aminci.

A yayin da ake ci gaba da fuskantar barazanar, hukumomi sun rika ba mazauna hulunan kariya tare da rakiyar jami’ai zuwa gidajensu domin daukar muhimman kayayyaki.

Iran ta illata Amurka a yaki da Isra'ila

A wani labarin, mun wallafa cewa kasar Iran ta bayyana irin nasarar da ta samu yayin yaki da Isra'ila da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo maganganu a duniya.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta illata Isra'ila, ta babbake wani babban kamfani a farmakin da ta kai

Iran ce ta harbo jirgin sama mara matuki na Amurka nau’in “LUCAS” a yankin Khorramabad da ke kasar bayan ta sha alwashin ba za ta bari a rika cin zarafinta ba.

Jami’an tsaro sun ce sun kama tare da lalata jirgin, amma Amurka ba ta tabbatar da lamarin ba har zuwa lokacin wannan rahoton duk da ana ci gaba da gwabza yakin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng