Amurka Ta Ci Karo da Cikas, Iran Ta Illata Ta a Yakinta da Kasar Isra’ila

Amurka Ta Ci Karo da Cikas, Iran Ta Illata Ta a Yakinta da Kasar Isra’ila

  • Kasar Iran ta bayyana irin nasarar da ta samu yayin yaki da Isra'ila da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo maganganu a duniya
  • Iran ce ta harbo jirgin sama mara matuki na Amurka nau’in “LUCAS” a yankin Khorramabad da ke kasar
  • Jami’an tsaro sun ce sun kama tare da lalata jirgin, amma Amurka ba ta tabbatar da lamarin ba har zuwa lokacin wannan rahoton

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Hukumomin Iran sun bayyana cewa sun harbo wani jirgin sama mara matuki na Amurka a yakin da ake yi.

An harbo jirghin ne mai suna “LUCAS” a birnin Khorramabad da ke lardin Lorestan, kamar yadda wasu rahotanni a Iran suka ruwaito.

Iran ta illata Amurka a yaki da Isra'ila
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Donald Trump na Amurka. Hoto: Anadolu Ajansi, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Jami’ai sun ce dakarun tsaro na yankin ne suka tare jirgin tare da lalata shi gaba daya, sai dai ba su bayar da karin bayani kan yadda aka gudanar da aikin ba, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta bar boye boye, ta bayyana adadin waɗanda suka jikkata a yaki da Iran

Yaushe aka fara yakin Iran da Isra'ila?

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

A yanzu, an shafe sfiye da wata guda kenan ana yakin wanda aka fara tun a ranar 28 ga watan Faburairun shekarar 2026 da muke ciki.

Harin da aka kai a ranar farko a birnin Tehran ya yi sanadiyyar jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaro.

Daga bisani, Iran ta mayar da martani ta hanyar harin makaman linzami wanda ya jawowa Amurka da Isra'ila barna mai yawa.

Yanayin jirgin Amurka da Iran ta fasa

A halin yanzu, babu wata sanarwa daga mahukuntan Amurka da ta tabbatar da wannan ikirari na Iran, kamar yadda MSN ta ruwaito.

Jirgin “LUCAS” na daga cikin jiragen yaki marasa matuki masu araha, wanda ake kira “kamikaze” ko kuma makamin da ke shawagi kafin kai hari, domin yana kai hari ne ta hanyar fashewa da zarar ya bugi abin da aka nufa.

Kara karanta wannan

JNI ta fadi adadin Musulman da aka kashe a harin jihar Filato

An yi amfani da irin wannan jirgi a wasu hare-haren da Amurka ta kai a yankin, wanda ke nuna sauyi a salon yaki na zamani zuwa amfani da jirage masu saukin kudi da ake iya tura su da yawa domin kai hari.

Amurka dai na ci gaba da bayyana cewa tana samun nasara a yakin da ake yi kuma ta cimma wasu bukatunta game da afkawa Iran da ta yi.

Shirin da Iran ke yi wa sojojin Amurka

A wani labarin, an ji cewa Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi magana kan makircin kasar Amurka yayin da ake tsaka da yaki.

Ghalibaf ya ce sojojin kasar sun shirya karbar sojojin Amurka, yana zargin suna shirin kai hari a boye duk da ikirarin tattaunawa.

Ya soki Trump kan maganar sulhu da Iran, yana cewa Amurka na aika sakon zaman lafiya amma a gefe guda tana shirin kai farmaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.