Amurka Ta Kira Sunayen Ƙasashe 2 da Ke Taimaka wa Iran a Yaki da Isra'ila

Amurka Ta Kira Sunayen Ƙasashe 2 da Ke Taimaka wa Iran a Yaki da Isra'ila

  • Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya yi magana kan zargin wasu ƙasashen da ke taimakawa Iran a yakin da ake yi
  • Hegseth ya ce suna sane da yadda China da Rasha ke taimakawa Iran a yakin da ake ciki, kuma suna daukar matakan dakile wannan goyon baya
  • Rahotanni sun nuna cewa Rasha na bayar da bayanan sirri na kai hare-hare, yayin da China ke taimakawa Iran da fasaha domin inganta harba makamai masu linzami

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya sake yin magana game da taimakawa Iran da ake yi a yaki.

Hegseth ya bayyana cewa sojojin kasar sun san cikakkiyar rawar da China da Rasha ke takawa wajen taimakawa Iran a yakin da ake yi.

Kara karanta wannan

'Ba da mu ba': Iran ta sake gindaya sharudan tsagaita wuta a yaki da Isra'ila

Amurka ta yi magana kan taimaka wa Iran
Shugaba Vladimir Putin yana ganawa da Donald Trump. Hoto: Anadolu/Getty Images.
Source: Getty Images

Amurka ta koka kan taimakon Iran a yaki

Rahoton CBS News ya ruwaito Hegseth na cewa ba za su bayyana dukkan bayanai a bainar jama’a ba.

Sai dai ya ce suna daukar matakai na rage tasirin wannan taimako tare da tinkarar duk wata barazana kai tsaye.

Rahotanni sun nuna cewa Rasha na bayar da bayanan sirri kai tsaye domin taimakawa Iran wajen kai hare-hare, musamman amfani da hotunan tauraron dan Adam da bayanan nuni na hari.

Wani bincike ya nuna cewa China na taimakawa Iran da fasaha da tsarin GPS na BeiDou, wanda ke kara karfin harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki.

Amurka ta fadi yadda ta gano Rasha da China da ke taimakawa Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Getty Images

Yadda alakar China, Iran ta ke a baya

Tun shekarar 2021, an ce China ta bai wa Iran damar amfani da bayanan tsarin BeiDou, yayin da Amurka ta kakabawa wasu kamfanonin China takunkumi kan tallafawa Iran.

Masana sun ce China, Rasha da Iran na aiki tare domin kauce wa takunkuman kasashen yamma, tare da karfafa hadin gwiwar soji da fasaha a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Amurka ta sha alwashi, ta fadi abin da ba za ta bari Iran ta mallaka ba

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya bayyana cewa yana da tabbacin Rasha na bai wa Iran bayanan sirri domin taimaka mata kai hari, cewar The Washington Post.

Ya ce wannan hadin kai yana cikin muradin Rasha, yana mai jaddada cewa suna ba da cikakken goyon baya wajen taimakawa Iran a yakin yankin.

Rahotanni sun kuma ce ana shirin aikewa Iran da jiragen yaki marasa matuki daga Rasha, duk da cewa Kremlin ya musanta wannan batu yana mai cewa karya ne.

Haka kuma, wasu jami’an Amurka sun zargi kamfanonin China da samar da kayan fasahar kere-kere ga sojojin Iran, duk da cewa China ta karyata zargin tana mai cewa labarin bogi ne.

Jami'an Rasha sun gana da na Amurka

Tun farko, mun ba ku labarin cewa jami’an kasar Rasha sun je Amurka domin tattaunawa yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin kasashen Iran da kuma Isra'ila.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wannan shi ne karo na farko da aka.yi wannan taro tun bayan takaddamar yakin Ukraine da take yi da Rasha.

Kasar Rasha ta sha musanta zargin taimaka wa Iran, tana mai cewa rahotannin kafofin watsa labarai ƙarya ne da aka kirkire su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.