Yaƙi Ya Ɗau Zafi: Iran Ta Lissafa Manyan Kamfanonin Amurka 18 da Za Ta Farmaka
- Rundunar IRGC ta Iran ta lissafa manyan kamfanonin Amurka guda 18 wadanda za ta kai wa hari daga daren ranar Laraba, 1 ga Afrilun 2026
- Kamfanonin Google, Apple, Meta, da Microsoft na cikin jerin wadanda Iran ke zargi da taimakawa Amurka wajen gano bayanan sirrin sojojinta
- Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Isra'ila ta lalata kashi 70 na masana'antun karfe na Iran tare da rage karfin tattalin arzikinta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta fitar da gagarumin gargaɗi na kai farmaki kan manyan kamfanonin fasaha na ƙasar Amurka dake gudanar da ayyuka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Iran ya fitar a yau Talata, ta lissafa kamfanoni 18 a matsayin "halattattun wuraren kai hari ga sojoji."

Kara karanta wannan
Ba wasa: Iran ta yi luguden wuta kan Amurka da Isra'ila, ta farmaki muhimman wurare

Source: Getty Images
Iran za ta farmaki kamfanonin Amurka
Wadannan kamfanoni da Iran za ta farmaka sun hada da Boeing, Tesla, Meta, HP, Microsoft, Google, da Apple, kamar yadda rahoton The Wall Street Journal ya nuna.
Sanarwar ta bayyana cewa:
"Tun da babban abin da ake amfani da shi wajen tsara wa da gano wuraren kai hare-hare sune kamfanonin fasahar sadarwa da na basirar ɗan-adam (AI) na Amurka, daga yanzu waɗannan cibiyoyin sun zama wuraren harinmu."
Rundunar ta IRGC ta buƙaci dukkan ma'aikata da mutanen dake zaune kusa da ofisoshin waɗannan kamfanoni da su fice cikin gaggawa kafin lokacin da aka ɗiba na fara kai hare-haren.
Soja Iran sun bayyana cewa an tsara fara kai hare-haren ne daga ƙarfe 8:00 na dare agogon yankin a gobe Laraba, idan har aka ƙara kashe wasu shugabannin Iran.
Tasirin hare-haren Isra'ila kan Iran
A gefe guda, Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Isra'ila tana lalata abubuwan more rayuwa na Iran bi-da-bi domin durƙusar da gwamnatin ƙasar.
A zaman majalisar zartarwar kasar na yau Talata, shafin USA Today ya ruwaito Netanyahu ya na cewa:
"Mun lalata kashi 70 na ƙarfin sarrafa ƙarfen su, kuma ta hanyar amfani da makamai kaɗan, mun rage ƙarfin tattalin arzikinsu (GDP) da kashi 2 zuwa 3 cikin ɗari."
A cewar Firayim Ministan, wannan asara ta kai ta biliyoyin daloli, kuma lalata hanyoyin samar da makamashin Iran yana tsoratar da gwamnatin ƙasar ƙwarai da gaske tare da raunana ta.

Source: Getty Images
Rikicin mashigar Hormuz
Game da batun rufe mashigar ruwan Hormuz da Iran ta yi, Netanyahu ya bayyana cewa Amurka tana da ikon magance wannan matsalar ta hanyar amfani da ƙarfin soja idan ta ga dama, in ji rahoton The Jerusalem Post.
Ya ba da shawarar cewa za a iya ketare mashigar ta hanyar tura bututun mai da iskar gas daga Iran zuwa Isra'ila ta hanyar ƙasar Saudiyya domin tabbatar da kwararar makamashi zuwa duniya.
A halin yanzu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya nanata cewa jami'o'in Amurka da na Isra'ila ma ba za su tsira ba biyo bayan hare-haren da aka kai wa jami'o'in Tehran da Isfahan.
Barazanar kai hari jami'o'in Amurka
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Rundunar 'Islamic Revolutionary Guard Corps' ta Iran ta yi barazanar kai hari kan jami’o’in Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
IRGC ta gargadi malamai, ma’aikata da dalibai na jami’o’in Amurka da ke yankin su nisanci harabar jami’o’in da tazarar kilomita daya domin tsaron rayukansu.
Akwai jami’o’in Amurka da dama da ke da rassa a kasashen yankin Gulf, ciki har da Texas A&M University a Qatar da New York University a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Asali: Legit.ng

