Iran Ta Kara Karya Tarihi, Amurka Ta Shiga Matsalar da ba Ta Taba Gani ba cikin Shekaru 4

Iran Ta Kara Karya Tarihi, Amurka Ta Shiga Matsalar da ba Ta Taba Gani ba cikin Shekaru 4

  • Farashin galan daya na fetur ya haura Dala 4 a fadin Amurka yayin da kasar ke ci gaba da musayar wuta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Wannan ne karo na farko da galan din man fetur ya yi tashin gwauron zabi a Amurka cikin shekaru hudu, lamarin da ake dangantawa da yakin Iran
  • Lamarin na da tasiri a siyasa, domin karin farashin mai na iya shafar ra’ayin jama’a, musamman yayin da ake tunkarar zabuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Washington – Farashin man fetur a Amurka ya haura Dala 4 a kowanne galan guda, karo na farko cikin kusan shekaru hudu.

Ana ganin hakan ta faru ne sakamakon tashin hankalin da ke da alaka da rikicin Iran da kuma fargabar tangardar samar da mai a duniya.

Gidan mai a Amurka.
Allon farashin man fetur a wani gidan mai a birnin Chicago na kasar Amurka Hoto: Scott Olson
Source: Getty Images

Fetur ya kara tsada a kasar Amurka

Kara karanta wannan

Shugaba Pezeshkian ya gano masu goyon bayan Iran a yaki da Amurka, ya aika masu sako

Daily Trust ta ruwaito cewa bayanai daga Kungiyar Masu Motoci ta Amurka (AAA) sun nuna cewa matsakaicin farashin kowane galan na fetur ya kai $4.018, daga kasa da $3 da aka samu a karshen watan Fabrairu, 2026.

Wannan shi ne mafi tsadar farashin fetur da aka samu tun watan Agustan 2022, kamar yadda Hukumar Makamashi ta Amurka ta tabbatar.

Me ya jawo tsadar fetur a Amurka?

Karin farashin na da nasaba da matakan soja da Shugaba Donald Trump ya dauka kan Iran, wanda ya jefa kasuwar makamashi cikin rashin tabbas a fadin duniya.

Haka kuma, rikice-rikicen da suka shafi mashigar ruwa ta Hormuz, wanda kusan kashi daya bisa biyar na man duniya ke bi ta cikinsa, sun kara dagula lamarin.

Matakan da Iran ta dauka wajen takaita zirga-zirga a wannan mashigi sun kara tayar da fargabar karancin mai, lamarin da ya sa farashin kowace gangar mai ya haura Dala 100, in ji rahoton Al-Jazeera.

Jihohi mafi tsadar mai a kasar Amurka

Farashin mai bai tsaya daidai a duk fadin Amurka ba, sai dai wasu jihohi sun fi shan wahala saboda yadda kowane galan ya kara tsada. Jihohi uku da lamarin ya fi shafa su ne:

Kara karanta wannan

Bayan Amurka, Trump zai tafi Venezuela neman takarar shugaban kasa

1. California – Dala 5.88 a kowane galan

2. Hawaii – Dala 5.45 kowane galan

3. Washington – Dala 5.34 kowace galan.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: @DonaldJTrump
Source: Getty Images

Ana ganin karin farashin mai zai kara kuntatawa mutanen Amurka, musamman yayin da lokacin tafiye-tafiye na bazara ke karatowa.

Ko da yake Amurka na samun mafi yawan man da take amfani da shi daga Canada da Mexico, tsarin kasuwar makamashi na duniya yana nufin duk wata matsala a wani yanki na iya shafar farashi a ko’ina.

Amurka ta cire takunkumi kan man Iran

An ji cewa gwamnatin Amurka ta cire takunkumi kan gangar mai miliyan 140 da ya fito daga kasar Iran a wani mataki na kokarin daidaita farashin mai a kasuwar duniya.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Shugaba Dinald Trump ta ba Iran lasisi na wucin gadi domin sayar da man da ke cikin tankokin jiragen ruwa a teku.

Amurka ta shafe shekaru tana kakaba takunkumi kan man Iran lokaci zuwa lokaci, kuma gwamnatin Trump ta hana sayar da man kasar tun bayan da ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Tehran

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262