Iran Ta Dauki Zafi, Ta Farmaki Muhimman Wuraren Amurka da Isra'ila
- Yakin da ake gwabzawa tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya na kara daukar zafi
- Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kaddamar da hare-hare masu zafi kan Amurka da Isra'ila
- IRGC ta bayyana cewa ta farmaki muhimman wurare hare-haren da ta kai, inda ta nuna cewa ga cikin akwai wuraren ajiye jirage marasa matuka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta kai hari kan muhimman wuraren Amurka da Isra'ila.
Rundunar IRGC ta ce ta farmaki cibiyoyin kula da yaki Amurka da Isra'ila, wuraren ajiye jirage marasa matuƙa da maboyar matuƙan jirgi a cikin sababbin hare-haren makamai masu linzami da ta kai kan sansanonin sojojinsu a yankin.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce hakan na kunshe ne a cikn wata sanarwa da IRGC ta fitar a ranar Litinin, 30 ga watan Maris 2026.
Wadanne wurare IRGC ta farmaka?
A cikin sanarwar, IRGC ta ce ta farmaki wuraren ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu dogon zango a matsayin ɓangare na jerin hare-hare na 87 na samamen Operation True Promise 4.
Ofishin hulda da jama'a na IRGC ya bayyana cewa an yi amfani makamai masu linzami waɗanda suka haɗa da nau'ikan Emad, Qiam, da Khorramshahr-4 tare da jirage marasa matuƙa, rahoton tashar Tass ya tabbatar da hakan.
Ta bayyana cewa makaman sun sauka a "cibiyoyin kula da yaki, wuraren ajiye jirage marasa matuƙa, ma'ajiyar makamai, da wuraren buya na dakarun soji da matuƙan jirgin ta'addancin Amurka da Isra'ila a yankuna daban-daban" yadda ya kamata.
Iran za ta ci gaba dakai hare-hare
A cewar sanarwar ta IRGC, hare-haren sun sauka sansanonin Amurka guda biyar a yankin, da kuma wuraren sojoji a kudanci, tsakiya, da Arewacin yankunan Isra'ila, ciki har da Haifa Bay, Kiryat Shmona, Tel Aviv, Be’er Sheva, Dimona, al‑Kharj, Jufair da sauran wurare.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"Wannan haɗaɗɗen samamen, wanda ke gudana ba kakkautawa kuma mataki-mataki, ya fara ne tun cikin dare kuma har yanzu ana nan ana gudanar da shi."

Source: Twitter
Iran ta yi Allah wadai da harin Isra'ila
IRGC ta jaddada cewa sansanonin Amurka da dakarunta a yankin, da kuma "cibiyoyin soja da na tsaro" na Isra'ila, halattattun wuraren hari ne ga Iran.
A lokaci guda kuma, sanarwar ta IRGC ta yi Allah-wadai da harin da Isra'ila ta kai kan wata masana'antar tace ruwa a ƙasar Kuwait, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da ya sabawa doka.
IRGC ta buƙaci ƙasashen yankin Yammacin Asia da su kasance cikin shiri da lura da makircin Amurka da Isra'ila, wanda ke neman dagula zaman lafiya da ruguza yankin."
Kasar Iran ta gargadi Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Ghalibaf, ya aika da sakon gargadi ga Amurka.
Ghalibaf ya yi gargaɗin cewa sojojin Iran suna jiran zuwan dakarun Amurka domin “ƙona su” da kuma hukunta abokan hulɗarsu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban majalisar dokokin ya ce, Iran ba za ta zauna sakaka sojojin Amurka sun kawo mata hari har gida ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


