Pakistan Ta Faɗi Matakin da ake a Ƙoƙarin Sulhu tsakanin Amurka da Iran

Pakistan Ta Faɗi Matakin da ake a Ƙoƙarin Sulhu tsakanin Amurka da Iran

  • Pakistan ta ce za ta karɓi bakuncin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ana ci gaba da tattaunawa kuma suna tafiya yadda ya kamata duk da yana kara shirin yaki
  • Iran ta yi barazanar kai hari kan sojojin Amurka da abokan hulɗarsu a yankin matuƙar ana ci gaba da kai mata farmaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Pakistan – Gwamnatin Pakistan ta sanar da cewa za ta karɓi bakuncin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, duk da cewa har yanzu babu cikakken bayani daga bangarorin biyu.

Ministan harkokin wajen Pakistan, Ishaiq Dar, ya ce ƙasarsa na alfahari da amincewar da Amurka da Iran suka nuna mata wajen taimaka wa tattaunawar.

Kara karanta wannan

Iran ta tanadi dakaru miliyan 1 a shirin yin gaba da gaba da sojojin Amurka

Pakistan ta shirya shiga tsakanin Amurka da Iran
Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, Jagoran addini na Iran Mojtba Khamenei Hoto: @CMShehbaz/Sayyid Mojtaba Khamenei
Source: Twitter

CBS ta wallafa cewa Pakistan ta bayyana fatan za a samu nasarar shawo kan matsalolin da suka addabi Gabas ta Tsakiya.

Pakistan ta magantu kan sulhun Amurka da Iran

AP News ta ruwaito cewa Ishaq Dar, ya bayyana halin da ake ciki awata ganawa da manyan jami’an diflomasiyya daga Turkiyya, Masar da Saudiyya a Islamabad.

Ya ce:

“Pakistan na farin ciki cewa bangarorin biyu sun nuna amincewa da ita. Zai zama abin girmamawa a gare mu mu karɓi bakuncin tattaunawa mai ma’ana a cikin kwanaki masu zuwa.”

Sai dai daga bisani jami’an sun bar ƙasar, duk da cewa an shirya ci gaba da tattaunawar a ranar Litinin.

Shugaban Amurka ya ce ana magana da Iran
Shugaban Amurka Donald J Trump a ofis Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Shugaban Amurka, Donald Trump, bai yi magana kai tsaye kan tattaunawar da za a yi a Pakistan ba, amma ya bayyana cewa ana tattaunawa da Iran kuma suna samun ci gaba sosai.

Ya ce:

“Muna yin kyau sosai a wannan tattaunawa.”

Kara karanta wannan

Ana zargin Rasha ta kusa kammala aika jiragen yaƙi marasa matuƙa ga Iran

Trump ya yi magana kan sulhu da Iran

Da aka tambaye shi ko Iran ta amsa shirin tsagaita wuta mai bukatu 15 da Amurka ta gabatar, Trump ya ce sun amsa kuma sun amince da yawancin abubuwan da aka gabatar.

Ya kara da cewa:

“Sun ba mu mafi yawan abubuwan da muka nema.”

Sai dai bai yi karin bayani ba. Rahotanni sun nuna cewa Pakistan na taka rawa a matsayin mai shiga tsakani, sakamakon kyakkyawar alakar da take da ita da Amurka da kuma Iran, bayan makonni na tattaunawa a ɓoye.

A gefe guda, shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya yi watsi da batun tattaunawar da za a yi a Pakistan, yana mai cewa magana ce kawai. A

Abin da zai kai sojojin Amurka Iran

A baya, kun samu labarin cewa wani rahoto ya binciko dalili na biyu da ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ke nazarin kai farmakin soja ta ƙasa a Iran.

Kara karanta wannan

A karshe, Trump ya samu kasashe 3 da za su taimaka ya shawo kan Iran

Rahotanni sun ce har yanzu ba a yanke hukunci na ƙarshe a kan al'amarin ba, amma ana fargabar haɗarin da sojojin Amurka za su fada matuƙar suka shiga Iran

Masana sun gargadi cewa wannan aiki na iya jawo ƙarin rikici a yankin yayin da Iran ta yi shirin tunkarar duk masu kai mata hari da abokan hulɗar Amurka da Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng