Iran Ta Shaidawa Amurka Tanadin da Ta Yi wa Sojojin da za Su Kutso cikin Kasarta

Iran Ta Shaidawa Amurka Tanadin da Ta Yi wa Sojojin da za Su Kutso cikin Kasarta

  • Iran ta gargadi Amurka bayan bayanain bayyana shirinta na aika sojoji su shiga cikin ƙasar da karfin tsiya
  • Rundunar IRGC ta yi barazanar kai hari kan jami’o’in Amurka da Isra’ila a yankin domin daukar fansa
  • Haka kuma, ta sanar da Donald Trump shirin da ta yi wa sojojin ƙasarta matukar suka yi gangancin shiga Iran

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Iran – Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi kakkausar gargadi ga Amurka kan yiwuwar kai farmakin ƙasa, inda ya ce ba za su lamunta ba.

Ghalibaf ya yi gargaɗin cewa sojojin Iran suna jiran zuwan dakarun Amurka domin “ƙona su” da kuma hukunta abokan hulɗarsu a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta gargaɗi Amurka kan shirin aika mata sojoji
Mai magana da yawun IRGC Ebrahim Zolfaghari, wasu daga cikin sojojin Amurka Hoto: Irani Force/1st Infantry Division
Source: Facebook

CBS ta wallafa cewa Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce, Iran ba za ta zauna sakaka sojojin Amurka sun kawo mata hari har gida ba.

Kara karanta wannan

Bayan kwadayin man fetur, an gano abin da zai kai sojojin Amurka cikin Iran

Shirin Iran kan sojojin Amurka

The Times of India ta ruwaito Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce ƙasarsa ba za ta raga wa sojojin Amurka ba.

Ya ce:

“Sojojinmu suna jiran zuwan Amurkawa a ƙasa domin su fuskanci hukunci mai tsanani.”

Ya ƙara da cewa Iran na ci gaba da harba makamai, yayin da shirinta na soja ke ƙara ƙarfi bayan Amurka da Isra'ila sun ci gaba da kai mata hari.

Ghalibaf ya kuma yi watsi da shirin sulhu mai bukatu 15 da ake zargin Donald Trump ke ƙoƙarin aiwatarwa ta hannun Pakistan, inda ya bayyana shi a matsayin burin Amurka kawai.

Iran ta ce sojojin Amurka za su gane kurensu
Motar yaki da wasu sojojin Amurka Hoto: 1st Infantry Division
Source: Facebook

Ya ce:

"Matukar Amurka na neman mu miƙa wuya, martaninmu a bayyane yake—ba za mu taɓa yarda da wulakanci ba.”

Rundunar sojin Iran ta yi barazana ga Amurka

A gefe guda kuma, rundunar IRGC ta yi barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin ilimi na Amurka da Isra’ila a yankin.

Kara karanta wannan

Yaƙi ya kacame, sojojin Amurka na shirin kutsa wa cikin Iran

Ta bayyana cewa za su zama halastattun wuraren hari idan Amurka ba ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa jami’o’in Iran ba.

Rundunar ta bukaci a kwashe ɗalibai da ma’aikata daga irin waɗannan cibiyoyi tare da umartar su su nisanta aƙalla kilomita ɗaya daga wuraren din tsira da rayukansu.

Rahotanni sun nuna cewa jami’o’i da dama sun fara ɗaukar matakan kariya. Jami’ar American University of Beirut ta sanar da cewa za ta koma koyarwa ta yanar gizo.

Amurka na son kwashe sinadarin Iran

A wani labarin, kun ji cewa wani rahoto ya bayyana dalili na biyu da ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ke nazarin kai farmakin soja ta ƙasa zuwa ƙasar Iran.

Duk da har yanzu ba a yanke hukunci na ƙarshe a kan al'amarin ba, amma ana fargabar haɗarin da sojojin Amurka za su fada matuƙar suka yi wa Iran kutse zuwa cikin ƙasarta.

Masana sun gargadi cewa wannan aiki na iya jawo ƙarin rikici a yankin yayin da Iran ta yi shirin tunkarar duk masu kai mata hari da ƙone sojojin da ake sa ran tura mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng