Bayan Kwadayin Man Fetur, An Gano Abin da zai Kai Sojojin Amurka cikin Iran
- Wani rahoto ya binciko dalili na biyu da ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ke nazarin kai farmakin soja ta ƙasa a Iran
- Har yanzu ba a yanke hukunci na ƙarshe a kan al'amarin ba, amma ana fargabar haɗarin da sojojin Amurka za su fada
- Masana sun gargadi cewa wannan aiki na iya jawo ƙarin rikici a yankin yayin da Iran ta yi shirin tunkarar duk masu kai mata hari
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America –Shugaban Amurka, Donald Trump, na duba yiwuwar kaddamar da wani farmakin soja bayan yakin Gabas ta Tsakiya na ƙara tsananta.
Wani rahoto ya gano Trump na son a kai harin domin kwashe kusan fam 1,000 na sinadarin uranium da ake hada makamin nukiliya da shi daga ƙasar Iran.

Source: Facebook
Al-Jazeera ta wallafa cewa rahoton ya bayyana cewa wannan aiki na da matuƙar wahala, kuma zai iya sa sojojin Amurka shiga cikin ƙasar Iran na tsawon kwanaki ko ma fiye da haka.
Sojojin Amurka za su shiga Iran
Anadolu Ajansi ta wallafa cewa majiyoyi sun ce har yanzu Trump bai yanke hukunci na ƙarshe a kan lamarin ba, yana ci gaba da auna haɗarin da irin wannan aiki zai iya haifar wa sojojin Amurka.
Ana duba yiwuwar wannan aiki ne a matsayin wani mataki na hana Iran haɓaka makaman nukiliyar da Amurka ke zargin tana haɗa wa.
Rahoton ya ce Trump na iya amincewa a kwashe sinadarin uranium ɗin ta ƙarfin tsiya idan ba a samu yarjejeniya ta tattaunawa ba.

Source: Getty Images
Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce:
“Alhakin ma’aikatar tsaro ne ta shirya dukkanin hanyoyin da za su bai wa shugaban ƙasa zaɓi da yawa a yakin.”
Ta ƙara da cewa hakan ba yana nufin shugaban ya yanke hukunci ba a kan batun tura sojojin ta ƙasa ba ne.
Iran: Trump ya ƙwallafa rai kan Uranium
An ce ana zargin uranium ɗin na ajiye ne a muhimman wurare, daga ciki har da wani rami ƙarƙashin ƙasa a cibiyar nukiliya ta Isfahan da kuma wani ma’ajiya a Natanz.
Masana sun bayyana cewa duk wani yunƙuri na kwashe uranium ɗin da ƙarfi zai kasance mai matuƙar wahala da haɗari, kuma zai iya jawo martani daga Iran tare da tsawaita rikicin.
Tsohon janar, Joseph Votel, ya ce:
“Wannan ba irin aikin da za a shiga a fita cikin sauƙi ba ne.”
Rahoton ya ce aikin zai buƙaci sojojin Amurka su shiga cikin Iran duk da barazanar jiragen yaƙi marasa matuƙa, makamai masu linzami da harbi ta ƙasa.
Haka kuma za su tsare wuraren sannan ƙwararru su nemo uranium ɗin su kwashe shi duk da barazanar da za su fuskanta.
An bayyana cewa uranium ɗin na cikin akwatuna na musamman guda 40 zuwa 50, waɗanda za a ɗora a manyan motocin kariya kafin a ɗauke su ta sama zuwa waje.
Sojojin Amurka za su kutsa cikin Iran
A wani labarin, mun wallafa cewa yakin da Amurka da Isra'ila suka jawo a Gabas ta Tsakiya bayan kashe jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei na shirin ƙara ƙazanta.
Wani rahoto ya bankaɗo cewa Amurka na shirin turo sojoji domin kai hare-haren ƙasa a Iran na tsawon makonni yayin da Trump ke barazanar kwashe danyen man fetur da ke ƙasar.
Ana sa ran hare-haren ba za su kai ga cikakken mamaya ba, sai dai farmaki na musamman a wasu muhimman wurare domin kwashe ma'adanan da za su kai su can.
Asali: Legit.ng


