Kasar Iran Ta Illata Isra'ila, Ta Babbake wani Babban Kamfani a Farmakin da Ta Kai

Kasar Iran Ta Illata Isra'ila, Ta Babbake wani Babban Kamfani a Farmakin da Ta Kai

  • Wani Kamfani a Isra'ila ya tabbatar da cewa an kai hari masana’antarsa a kudancin kasar da makami daga Iran
  • Gobara ta tashi a yankin masana’antu na Ne’ot Hovav bayan harin, inda jami’an kashe gobara 34 suka yi kokarin shawo kan lamarin
  • Hukumomi sun ce an shawo kan gobarar, duk da lalacewar gini, yayin da aka gargadi jama’a su guji yankin saboda sinadarai masu hadari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Kamfanin Isra’ila mai kera magungunan kashe kwari, ADAMA, ya ce an kai hari ga masana’antarsa.

Lamarin ya faru ne a yankin da ke Makhteshim a kudancin ƙasar a ranar Lahadi 29 ga watan Maris, 2026.

Harin Iran ya lalata kamfani a Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Ya bayyana cewa makami mai linzami daga Iran ko kuma tarkacen wanda aka tare ne ya bugi wurin, amma babu wanda ya jikkata a lamarin, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

Gargadi mai tsauri da Trump ya yi ga kasar Iran kan sharudansa na zaman lafiya

Abin da kamfanin ya ce game da harin

Kamfanin ya ce har yanzu ba a tantance girman barnar da aka yi ga masana’antar ba, duk da rahotannin faruwar fashewa da gobara.

Hukumar kashe gobara ta Isra’ila ta ce gobara ta tashi a yankin masana’antu mai dauke da kamfanonin sinadarai da dama bayan harin makami.

An ce tarkacen makamin da aka tare ne ya haddasa gobarar, wanda ya jawo damuwa saboda hadarin sinadarai masu illa a yankin.

Hukumar ta bukaci jama’a su guji yankin Ne’ot Hovav, tana mai cewa akwai hadarin sinadarai, yayin da jami’ai 34 ke aiki wajen kashe gobarar.

Ta kara da cewa babu wata barazana ga jama’a idan sun kasance fiye da tazarar mita 800 daga yankin masana’antu da abin ya shafa, cewar Al Jazeera.

Hotuna da bidiyo sun nuna wuta mai girma da hayaki baki mai yawa, yayin da jami’an ke kokarin hana yaduwar gobarar zuwa sauran wurare.

Daga baya, hukumomi sun ce an shawo kan lamarin gaba daya, duk da cewa wani gini ya lalace gaba daya sakamakon gobarar.

Kara karanta wannan

Matakai 4 da Najeriya ta dauka bayan fara yakin Iran, Amurka da Isra'ila

Jami’an kashe gobara sun ci gaba da aikin kashe sauran wutar da kuma sanyaya wurin domin hana sake tashi nan gaba.

Kamfanin Isra'ila ya tabbatar da lalata shi da Iran ta yi
Sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Yadda Iran ta gano makamai masu linzami

Tun farko, rundunar sojin Isra’ila ta ce ta gano makamai masu linzami da aka harba daga Iran zuwa cikin kasar a ranar Lahadi.

An ce an yi harba makamai sau da dama, amma kafin gobarar da ta tashi, babu rahoton asarar rayuka ko jikkata mutane.

Yankin Ne’ot Hovav yana kusan kilomita 13 daga Beer Sheva, wanda shi ne babban birni mafi girma a kudancin Isra’ila.

A yankin akwai sansanonin soji da dama, wanda ke kara nuna muhimmancin wurin a fannin tsaro da harkokin masana’antu.

Hormuz: Martanin Iran ga kawayen Amurka

Mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta yi martani ga kasashe a duniya bayan barazanar Amurka game da rufe mashigar Hormuz da aka yi.

Iran ta ce mashigan Hormuz a bude yake ga jiragen ruwa, sai dai wadanda ke da alaka da abokan gabanta, yayin da rikici ke kara tsananta.

Jami’in Iran Ali Mousavi ya bayyana cewa jiragen da ba na makiya ba za su iya wucewa idan sun hada kai da Tehran wajen tsaro da aminci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com