Abin Ya Wuce Tunanin Amurka, an ‘Gano’ Girman Tallafi da Rasha Ke ba Iran

Abin Ya Wuce Tunanin Amurka, an ‘Gano’ Girman Tallafi da Rasha Ke ba Iran

  • Kasashen Turai sun bayyana zarge-zargensu kan Rasha game da tuhumarta da ake yi na taimaka wa Iran a yakin da ake yi
  • Rahotanni sun nuna cewa Rasha na bai wa Iran bayanan leken asiri da fasahar yaki, ciki har da amfani da jiragen marasa matuki
  • Sai dai Marco Rubio ya rage muhimmancin hadin gwiwar, yana cewa ba ta kawo cikas ga ayyukan Amurka ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Kasashen Turai sun yi zarge-zarge masu karfi kan rade-radin cewa Rasha na taimakawa kasar Iran a yakin da ake yi.

Kasashen sun bayyana wa jami’an diflomasiyyar Amurka cewa Rasha na taimakawa Iran a yakin da ake yi fiye da yadda Amurka ke bayyana a bainar jama’a.

An sake zargin Rasha da taimakawa Iran a yaki da Isra'ila
Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran da Vladimir Putin na Rasha. Hoto: Alexander KAZAKOV/POOL/AFP.
Source: Getty Images

Sun kuma jaddada cewa yakin Ukraine da na Iran suna da alaka, sakamakon hadin gwiwa tsakanin Rasha da Iran a bangaren soja, cewar rahoton CBS News.

Kara karanta wannan

Houthi da ta gwabza da Amurka a baya za ta taya Iran yaki, ta fadi sharuda

Yakin Iran/Isra'ila: Zargin da ake yi wa Rasha

An sha zargin Rasha na taimakawa Iran a yakin da ake yi tsakaninta da Isra'ila wanda ya jawo asarar rayuka da dama daga dukan bangarori.

Shi ma shugaban Ukraine, Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy ya yi magana kan yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Zelenskiy ya ce kasarsa ta samu hujja karara cewa Rasha na bai wa Iran bayanan sirri, lamarin da zai kara tsawaita rikicin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban ya ce Rasha na amfani da fasahar tattara bayanan sigina da hadin gwiwa da wasu kasashen yankin domin taimaka wa Iran wajen kai hare-hare.

Kasasehn Turai sun sake taso Rasha a gaba game da yakin Iran
Sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Ana zargin Rasha na tallafa wa Iran

Wani jami’i daga Birtaniya ya ce hadin gwiwar tsaro tsakanin Rasha da Iran ya karu sosai a ‘yan shekarun nan, inda Iran ta taimaka da fasaha da aka gani a hare-haren Gabas ta Tsakiya.

Sai dai ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya rage muhimmancin wannan hadin gwiwa, yana cewa ba ta kawo wani cikas ga ayyukan Amurka ba.

Kara karanta wannan

Tchiani ya tsoma baki a yakin Iran da Isra'ila, yana zargin an kulla wa Nijar makirci

Ya kara da cewa Amurka na sane da dukkanin hulda tsakanin kasashen, kuma tana daukar matakan da suka dace domin kare muradunta, cewar The Guardian.

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya bayyana dangantakar da ke tsakanin Rasha da Iran a matsayin “hadin gwiwa mai bangarori biyu.”

Ya ce:

“Akwai dalilai da ke nuna cewa yanzu Rasha na tallafawa kokarin sojan Iran, wanda da alama an fi karkata shi kan wasu hare-hare da suka shafi muradun Amurka.”

Rasha ta yi jimamin mutuwar Larijani

A baya, mun ba ku labarin cewa kisan da Isra'ila ta yi wa babban jagoran tsaron kasar Musulunci ta Iran, Ali Larijani ya ja hankalin shugabannin kasashen duniya.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya nuna alhini tare da aika sakon ta'aziyya ga jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei kan wannan babban rashi.

Shugaba Putin ya bayyana Larijani a matsayin “abokin kwarai,” na Rasha, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kawance kasar da Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.