Mayakan Houthi Sun Shigawa Iran Yaki, Sun Yi Ruwan Wuta a Isra'ila

Mayakan Houthi Sun Shigawa Iran Yaki, Sun Yi Ruwan Wuta a Isra'ila

  • Rikicin Gabas ta Tsakiya na ƙara tsananta yayin da mayakan Houthi da ke kasar Yemen suka fara kai harin makamai kan Isra’ila
  • Matakin na nuna yiwuwar faɗaɗa yaƙin da ke gudana da kuma ƙarin tashin hankali a Gabas ta Tsakiya da zai iya shafar duniya
  • Tun da farko dai dama Hotuthi ta yi gargadi tare da kafa sharudan guda uku da za su iya jawowa ta shiga yakin kafin fara kai hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yemen - Mayakan Houthi na Yemen sun kai hari kan Isra'ila da jerin makamai masu linzami masu nisa, wanda shi ne karo na farko tun bayan fara yaƙin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran.

Mai magana da yawun sojin Houthis, Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar da harin a ranar Asabar ta kafar talabijin ta Al Masirah.

Kara karanta wannan

Yaki zai fadada: Kasar Afrika 1 tilo ta fito za ta taya Isra'ila yakar Iran

Harin Houthi zuwa Isra'ila
Makamin da Houthi ta harba zuwa Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Houthi za ta kai hare-hare Isra'ila

Bayan harin da Houthi ta kai Isra'ila, Al-Jazeera ta rahoto Saree ya ce hare-haren za su ci gaba har sai an cimma manufofin da aka ayyana.

Bayanin da ya yi ya nuna cewa za su cigaba da yaki har sai an dakatar da hare-hare kan dukkanin bangarorin da suke cikin gwagwarmayar.

Isra'ila ta tabbatar da harin Houthi

Rahoton BBC ya nuna cewa rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da harin, inda ce ta tare makami mai linzami guda ɗaya daga cikin makaman.

Harin ya zo ne awanni kaɗan bayan da Saree ya nuna a wata sanarwa a ranar Juma’a cewa suna shirin shiga wannan yaƙi da ya girgiza yankin Gabas ta Tsakiya da kuma tattalin arzikin duniya.

Saree ya ce an harba makamai masu linzami da dama da nufin kai hari kan wasu muhimman cibiyoyin soja na Isra’ila a Kudancin ƙasar.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban kamu, an gano mutane da ke yada sirrinta ga makiya a yaki da Isra'ila

Kakakin sojojin Houthi
Birgediya Janar Yahya Saree da ke magana da yawun sojojin Houthi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An ji karar motocin gargadi a yankin Beersheba da kuma kusa da cibiyar binciken makamashin nukiliya ta Isra’ila sau uku daga daren Juma’a zuwa safiyar Asabar, yayin da Iran da Hezbollah ke ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila.

Tasirin hare-haren Houthi a baya

Hare-haren da kungiyar ke kai wa jiragen ruwa a lokacin yaƙin Isra’ila da Hamas sun kawo cikas ga zirga-zirgar kasuwanci a Tekun Bahar Maliya, inda kayayyakin da kudinsu ya kai kusan Dala tiriliyan 1 ke bi duk shekara.

Daga Nuwamba 2023 zuwa Janairu 2025, mayakan Houthi sun kai hare-hare kan fiye da jiragen ruwa 100 da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka, inda suka nutsar da jirage biyu tare da kashe matuƙan jirgi hudu.

Uganda za ta taya Isra'ila yaki

A wani labarin, kun ji cewa babban hafsun kasar Uganda, Muhoozi Kainerugaba ya ce za su taimaka wa Isra'ila a yakin da ta ke da Iran.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: An yi wa jirgin Isra'ila ruwan wuta bayan tura shi kai hari

Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa ba za su zuba ido a ruguza Isra'ila ba, ya ce duk abin da ya kamata su yi wajen taimakawa kasar za su yi.

Hafsun sojan ya kawo dalilai na tarihi inda ya nuna cewa kasar Isra'ila ta taimaki Uganda a shekarun baya a yaki da 'yan ta'adda.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng