'Yan tawayen Houthi sun kai hari sun ƙona jirgin saman kasar Saudiyya
- Yan tawayen Houthi da kasar Iran ke marawa baya sun kai hari a filin tashin jirage a Saudiyya a cewar dakarun kasar
- Wani jirgin daukan fasinjoji da ke filayen tashin jiragen ya kama da wuta sakamakon harin da yan tawayen suka kai
- Dakarun sojojin da ke yaki da yan tawayen ba su bayyana ko an samu salwantar rayyuka ba sakamakon harin
Wani jirgin farar hula ya kama da wuta sakamakon harin ranar Laraba da yan tawayen Houthi na Yemen suka kai a filin tashin jiragen sama da ke Kudancin Saudiyya, kamar yadda gamayyar masu yaki da masu tada kayan bayan suka sanar, The Punch ta ruwaito.
"Wasu ragwaye yan kungiyar masu tada kayan baya na Huthi sun kai harin ta'addanci a filin tashin jirage na Abha da ke Saudiyya," gidan talabijin na Al-Ekhbariya ya ce ya jiyo gamayyar na cewa.
"An yi nasarar kashe wutar da ta kama jiragen jigilar fasinjoji sakamakon harin na Huthi a filin tashi da saukan jiragen," ta kara da cewa.
DUBA WANNAN: Saki: Mata ta mayarwa miji sadakin N28,000 da ya biya yayin aurenta shekaru 7 da suka shude
Gamayyar sojojin bata bayyana ko an samu rasa rai ba ko kuma yadda aka kai harin duk da cewa a baya ta ruwaito cewa ta kama wasu jirage marasa matuka na yan tawayen.
Yan tawayen na Huthi da Iran ke marawa baya, kawo yanzu ba su dauki nauyin kai harin ba.
Amma akawai alamun cewa masu tada kayar bayan suna kara yawan hare-haren da suka kai wa Saudiyya da kuma dakarun Yemen bayan da Amurka ta cire kungiyar daga cikin jerin kungiyoyin ta'addanci a makon da ta gabata.
Amurka a ranar Juma'a ta sanar da majalisar niyar ta na cire kungiyar daga cikin jerin kungiyoyin ta'addanci da gwamnatin ta yi daf da saukan tsohon shugaba Trump.
Hakan na zuwa ne kwana daya bayan Shugaba Biden ya sanar da cewa Amurka za ta janye taimakon da ta bawa dakarun da Saudiyya ke yi wa jagoranci don yaki a Yemen.
A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.
Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng