Yaki zai Fadada: Kasar Afrika 1 Tilo Ta Fito za Ta Taya Isra'ila Yakar Iran

Yaki zai Fadada: Kasar Afrika 1 Tilo Ta Fito za Ta Taya Isra'ila Yakar Iran

  • Rahotanni sun nuna cewa kasar Uganda ta nuna alamun shiga yakin da ake a Gabas ta Tsakiya domin taya Isra'ila kai hare-haren soji Iran
  • Babban hafsun soja a kasar, Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa Isra'ila ta taimaka musu a baya, lokaci ya yi da za su rama alherin da aka musu
  • Hakan na zuwa ne yayin da aka shiga wata guda ana gwabza yaki da Iran bayan hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kaddamar a Tehran

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Uganda - Babban hafsan sojin Uganda, Muhoozi Kainerugaba, ya bayyana shirinsa na yaƙi tare da Isra'ila a rikicin da take yi da Iran.

Ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa, amma ya yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na lalata Isra’ila na iya sa Uganda ta shiga yaƙin.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Isra'ila na shirin rugujewa ana yakin Iran, an gargadi Netanyahu

Muhoozi Kainerugaba
Hafsun sojan Uganda, Muhoozi Kainerugaba. Hoto: @mkainerugaba
Source: Twitter

Kasar Uganda za ta taya Isra'ila yaki

Janar Kainerugaba ya wallafa saƙonni da dama a kafar sada zumunta ta X, inda ya ce ƙasarsa na iya shiga rikicin idan ya ƙara tsananta.

“Idan Isra’ila na buƙatar taimako, sai ta nemi hakan kawai. ‘Yan’uwanta na Uganda a shirye suke su taimaka,”

In ji Kainerugaba, wanda shi ne ɗan shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Museveni.

Dalilin Uganda na goyon bayan Isra'ila

Rahoton The Telegraph ya nuna cewa ya danganta goyon bayansa da alaƙar tarihi, yana mai tuna yadda Isra’ila ta taba taimakawa Uganda a baya.

Ya ce ɗan’uwan Benjamin Netanyahu, Yonatan Netanyahu ya mutu ne yayin jagorantar farmakin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Entebbe a shekarar 1976.

“Mu na son yaƙin Gabas ta Tsakiya ya ƙare yanzu,”

Inji shi

.“Duniya ta gaji da shi. Amma maganar cin nasara kan Isra’ila zai sa mu shiga yaƙin. Isra’ila na da ‘yancin wanzuwa kuma dole a dakatar da hare-haren da ake kai mata.”

Kara karanta wannan

Yan Isra'ila sun fara gajiya da halin Netanyahu, sun soke shi kan yaki da Iran

A wani saƙo da daga bisani aka goge, ya ce rundunar sojin Uganda za ta iya kwace Tehran cikin sa’o’i 72 ba tare da kai harin bam ba.

Benjamin Netanyahu a wajen taro.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rundunar sojin Uganda (UPDF) na da sojoji tsakanin 40,000 zuwa 45,000, ciki har da rundunar sojojin sama, a cewar gwamnatin kasar.

Ayyukanta na baya-bayan nan sun haɗa da tura sojoji 6,200 zuwa kasar Somalia, inda suka samu horo mai yawa daga Amurka.

Houthi za su taya Iran yaki

A wani labarin, kun ji cewa dakarun Houthi da ke Yemen sun sanar da cewa a shirye suke su shigar wa Iran yakin da ta ke da kasashe Isra'ila da Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Mai magana da yawun rundunar Houthi ya bayyana cewa za su shiga yakin ne da zarar wata kasa ta shigawa Isra'ila fadan da ake cigaba da yi.

Haka zalika kungiyar ta ce idan taga yakin ya kara tsananta za ta shiga ciki, duk da cewa bata fadi irin gudunmuwar da za ta ba Iran ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng