Trump na Shirin Kara Dagula Duniya, Ya Fadi Kasar da zai Afkawa da Yaki
- Yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump ke ta maganganu kan kawo karshen yakin da suke da Iran, ya fadi kasar da za su shiga a gaba
- Shugaba Trump ya yaba wa sojojin Amurka kan yadda suka shiga har kasar Venezuela suka kama shugaban kasar da matarsa suka tafi da su
- Rahotanni sun nuna cewa Trump ya yi magana ne yayin wani taro da aka gudanar a birnin Miami na kasar Amurka game da tattalin arziki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na cigaba da yi wa kasashen duniya barazana inda ya ke nuna cewa suna da karfin soja.
Trump ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun samu nasara sosai a Iran, inda ya yaba musu kan kama Shugaban kasar Venezuela da suka yi.

Source: Getty Images
Rahoton da kafar yada labarai ta Reuters ta wallafa ya nuna cewa Trump ya maimaita gargadin da ya yi wa kasar Cuba bayan saka mata takunkumi.
Donald Trump zai farmaki kasar Cuba
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Juma’a cewa “Cuba ce ta gaba” yayin wani jawabi a wani taron zuba jari a Miami, inda ya yi alfahari da nasarorin da sojojin Amurka suka samu a Venezuela da kuma Iran.
Duk da haka, Trump bai bayyana takamaiman abin da yake shirin yi game da Cuba ba, amma ya sha bayyana cewa yana ganin gwamnatin Havana, wadda ke fuskantar matsananciyar matsalar tattalin arziki, na dab da rushewa.
A ‘yan makonnin nan, gwamnatinsa ta bude tattaunawa da wasu bangarori na shugabancin Cuba, yayin da shi kansa Trump ya nuna yiwuwar amfani da karfin soja.
“Na gina rundunar soja mai ƙarfi sosai. Ba dole sai an yi amfani da ita ba. Amma wani lokaci dole ne a yi amfani da ita. Kuma Cuba ce ta gaba,”
Inji Trump a wajen taron.
Daga nan ya ce:
“Amma ku dauka kamar ba ku ji na faɗi hakan ba.”
Cuba na tattaunawa da Trump
A kwanakin baya, sShugaban Cuba, Miguel Diaz-Canel, ya amince cewa ƙasar na tattaunawa da Amurka domin kauce wa yiwuwar rikicin soja.

Source: Getty Images
Tattalin arzikin Cuba ya samu matsin lamba sosai sakamakon katsewar shigo da mai, wanda ƙasar ke dogaro da shi wajen samar da wutar lantarki da sufuri, musamman bayan sauye-sauyen da suka faru a Venezuela.
Tun da farko, Trump ya taɓa cewa Cuba na iya fuskantar abin da ya kira “karɓar iko cikin lumana,” kafin daga bisani ya ƙara da cewa hakan na iya zama ba cikin lumana ba.
Ga bidiyon bayanin Trump da Al-Jazeera ta wallafa a X:
Trump zai yi takara a Venezuela
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa zai iya yin takarar shugaban kasa a Venezuela.
Ya bayyana haka ne yayin wani taron ministoci da ya jagoranta a kasar, inda ministocinsa suka bayyana cewa an samu nasaori sosai a kasar Venezuela.
Trump ya yi maganar takara a Venezuela ne bayan kama shugaban kasar da sojojin Amurka suka yi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


