Tchiani Ya Tsoma Baki a Yakin Iran da Isra’ila, Ya Zargi Kulla Makirci Kan Nijar

Tchiani Ya Tsoma Baki a Yakin Iran da Isra’ila, Ya Zargi Kulla Makirci Kan Nijar

  • Shugaban Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya nuna damuwa kan rikicin Iran da Isra’ila, yana mai cewa yakin na iya haifar da karin rikici a duniya
  • Tchiani ya yi zargin cewa wasu ƙasashe na shirin amfani da wannan rikici domin kulla makirci da kai farmaki kan Nijar da abokanta
  • Ya bayyana cewa harin da Amurka da Isra’ila suka fara ya janyo asara mai yawa, yayin da Iran ta mayar da martani da harba rokoki masu haddasa barna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Niamey, Nijar - Shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahaname Tchiani ya tsoma baki game da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Tchiani ya nuna damuwa game da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Nijar na zargin shirya mata farmaki
Shugaban mulkin soja a Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani. Hoto: ORTN - Télé Sahel/AFP.
Source: Getty Images

Shugaban Tchiani ya bayyana haka yayin wani taro da aka gudanar wanda tashar RFI Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban kamu, an gano mutane da ke yada sirrinta ga makiya a yaki da Isra'ila

Yadda yakin iran da Isra'ila ya barke

Wannan na zuwa ne bayan yaki ya barke a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da kuma kasar Isra'ila.

Amurka da Isra'ila ne suka fara kai harin ne a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki wanda ya sanadiyyar rayuka da dama.

Yayin harin, jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya rasa ransa da wasu manyan jami'an tsaro a kasar.

Daga bisani, Iran ta mayar da martani inda ya ci gaba da harba makaman rokoki wanda ya jawo asara ga bangaren Amurka da Isra'ila.

Nijar ta magantu kan yakin Iran da Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Abin da Tchiani ya ce kan yakin Iran/Isra'ila

Yayin jawabinsa, Tchiani ya yi zargin cewa ana kulla manakisa kan farmaki a Nijar, Mali da Burkina Faso domin biyan bukatar wasu kasashe.

Shugaban ya ce wasu ƙasashe na neman yin amfani da damar yakin da ake yi domin afakawa Nijar.

Ya ce:

"Ba zan kammala wannan jawabi ba sai na tabo batun yankin Gabas ta Tsakiya da wasu kasashe da ke fama da yaki.

Kara karanta wannan

Yakin Iran/Isra'ila ya fara sauya salo, jami'ai daga Rasha sun dura a Amurka

"Wannan lamari dai yana daga mana hankali matuka musamman tattalin arzikinmu, yana daga mana hankali saboda yana shafar yan uwanmu."

Shugaban ya ce ya zama wajibi kasashensu su koyi darasi game da abin da ke faruwa, ka da su manta akwai manyan kasashe da dama masu mummunanr manufa.

"Za su iya amfani da wannan dama domin kaddamar da hare-hare a kan kasarmu, zan yi amfani da wannan dama domin kara jinjinawa al'ummarmu saboda tsayawa tsayin daka domin yaki da wannan mummunan manufa.
"Ba za mu taba bari makiya su zo su bata mana kasa ba, za mu karfafa kungiyar kasashenmu ta AES domin kare kai daga duk abin da zai cutar da mu."

- Abduorahamane Tchiani

Zarge-zargen Tchiani kan Faransa

Mun ba ku labarin cewa shugaban mulkin soja na jamhuriyyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya zargi Faransa da ba ‘yan ta’adda makamai da jiragen yaki.

Ya ce Faransa na kokarin hana hadin gwiwar kasashen Sahel (AES) samun nasara saboda yana kallonsu a matsayin barazana gare ta.

Tchiani ya ce makasudin Faransa shi ne hana kasashen Sahel mallakar albarkatun kasa bayan ta kwashe shekaru tana morarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.