Bayan Amurka, Trump Fa Fadi Kasar da zai Tafi Ya Nemi Shugaban Kasa

Bayan Amurka, Trump Fa Fadi Kasar da zai Tafi Ya Nemi Shugaban Kasa

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa zai tafi wata kasa domin neman zama shugabanta idan ya gama mulkin Amurka
  • Rahotanni sun bayyana cewa Trump ya fadi haka ne a yayin taron majalisar ministocin Amurka karo na 11 na wa’adinsa na biyu
  • Wasu daga cikin ministocin shugaban kasar sun yaba masa bisa matakan da ya ke dauka a kasashen duniya, inda suka ce yana kan daidai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janyo dariya daga jami’an gwamnatinsa bayan ya yi barkwanci game da abin da zai iya yi bayan kammala wa’adinsa a Fadar White House.

A bayanan da ya yi, Trump ya nuna cewa zai iya tafiya kasar Venezuela da ya kama shugabanta domin tsayawa takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Trump ya faɗi abin da Iran ta bukata a gare shi a yaki, ya kara mata wa'adin kwanaki 10

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa wasu daga cikin ministocin Trump sun yi karin bayani kan matakan da suke dauka a Venezuela.

Trump zai yi takara a Venezuela

A yayin taron majalisar ministoci na 11 na wa’adinsa na biyu a ranar Alhamis, Trump ya ce Venezuela na cikin mafi kyawun hali a tarihinta.

Hakan na zuwa ne bayan wani farmakin da sojojin Amurka suka kai a watan Janairun 2026 wanda ya kai ga kama shugabanta, Nicolás Maduro, tare da matarsa.

Royal News ta wallafa a Facebook cewa Donald Trump ya ce:

“A zahiri, ni ne wanda ya fi kowa farin jini. Wato bayan shugabanci a Amurka, ina ganin zan iya zuwa Venezuela in tsaya takarar shugaban ƙasa.”

Cikin dariya, Trump ya ce yana iya tsayawa takara da shugabar rikon ƙwarya ta ƙasar, Delcy Rodríguez, yana mai cewa:

“Wannan wata dama ce. Suna sona a Venezuela. Amma dai wata dama ce mai kyau.”

Kara karanta wannan

Ana zargin Rasha ta kusa kammala aika jiragen yaƙi marasa matuƙa ga Iran

Venezuela ta samu kudi sosai

Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa ƙasar ta samu karin kuɗin shiga daga sayar da mai a watanni biyu na farkon shekarar nan fiye da shekarar 2025.

A tsakiyar watan Fabrairun 2026, ministan makamashi, Chris Wright, ya ce kudin da Venezuela ta samu sun haura Dala biliyan 1.

Bayan harin, Amurka ta karɓi iko da fitar da man fetur na Venezuela, inda ake tura kuɗin zuwa wani asusun da Amurka ke kula da shi a Qatar, kafin daga bisani a aika su zuwa asusun da ma’aikatar kuɗi ta Amurka ke sarrafawa.

Shugaban Venezuela, Nicolás Maduro
Shugaba Nicolás Maduro da Amurka ta kama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rubio ya ce idan aka tura kuɗin ga gwamnatin Venezuela, za su taimaka wajen gudanar da ayyuka masu muhimmanci kamar tallafawa asibitoci da biyan malamai, yana mai jaddada cewa ba a sace su ba.

A martanin da ya yi, Trump ya ƙara da cewa:

“Mu ma muna samun kaso mai yawa,”

Kara karanta wannan

Gargadi mai tsauri da Trump ya yi ga kasar Iran kan sharudansa na zaman lafiya

Iran ta shirya karo da dakarun Trump

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ba zai sanar ba ko da zai tura sojojin kasa yaki a Iran.

A nata bangaren, Iran ta tanadi sojoji sama da miliyan 1 domin fafatawa da duk wani rukuni na sojoji da Donald Trump ya tura Tehran.

Hakan na zuwa ne yayin da aka shirin kai wata daya da fara yakin Amurka/Isra'ila da Iran da ya jawo asarar rayukan sojoji da fararen hula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng