Ba Sauki: Sojojin Amurka Sun Fara Tserewa daga Sansanoninsu saboda Harin Iran
- Sojojin Amurka sun tsere daga sansanoninsu zuwa otal-otal domin neman kariya daga makaman linzami na kasar Iran
- A ƙasar Kuwait, kusan dukkan sansanonin Amurka 13 sun koma kufai, abin da ya tilasta wa sojojin gudun hijira zuwa cikin birane
- Iran ta bukaci mazauna yankin Gabas ta Tsakiya da su tona asirin wuraren da sojojin Amurka ke buya domin kaddamar da hare-hare
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
A cikin mako na huɗu na gagarumin yaƙin da ake fafatawa a yankin Gabas Ta Tsakiya, dakarun Amurka sun fara tserewa daga sansanoninsu na soja zuwa otal-otal da gine-ginen ofisoshi na farar hula.
Wannan mataki ya biyo bayan jerin hare-haren ramuwar gayya da ƙasar Iran ta kai kan sansanonin sojin Amurka, lamarin da ya tilasta wa dubban sojoji guduwa domin neman maɓoya.

Source: Getty Images
Sojojin Amurka sun tsere daga sansanoninsu
Gidan jaridar New York Times ta ruwaito cewa kusan dukkan dakarun ƙasa na Amurka yanzu haka suna gudanar da irin salon nan na "aiki daga gida" bayan sun bar sansanoninsu.
Ban da matuƙan jiragen yaƙi da ma’aikatan da ke gyara jiragen dake kai hare-hare, sauran sojojin sun tsere tare da bazuwa a cikin birane daban-daban na yankin.
Rahoton ya nuna cewa dakarun sun nemi mafaka ne domin tsira da rayukansu daga hare-haren makamai masu linzami da Iran ke kai wa kan sansanoninsu.
Bayan tabbatar da tserewar sojojin, rundunar IRGC ta buƙaci mazauna yankin da su tona asirin duk wani sojan Amurka da suka gani ya nemi mafaka a cikinsu.
Iran ta nemi a fatattaki sojojin Amurka
Iran ta zargi Amurka da yin amfani da farar hula a matsayin garkuwa ta hanyar zama a cikin otal-otal dake tsakiyar birane, in ji rahoton MSN.

Kara karanta wannan
Trump ya juyo kan Najeriya, Amurka ta sake turo daruruwan sojoji, jiragen yaƙi ƙasar
Lt. Col. Ebrahim Zolfaghari, kakakin helkwatar Khatam Al-Anbiya, ya gargaɗi mutanen yankin da su nisanci duk wani gini da sojojin Amurka ke ciki domin amincin rayuwarsu.
A cewar Zolfaghari:
“Tun da yake an kakkabe dukkan sansanonin Amurka dake yankin, kwamandoji da sojojin Amurka sun gudu sun fake a maɓoyar da ba na soja ba.
"Muna roƙon mutanen ƙasashen yankin da su kai rahoton maɓoyarsu, sannan su buƙaci a fitar da Amurkawa daga yankin.”

Source: Getty Images
Illar hare-haren Iran a Gabas ta Tsakiya
Hare-haren Iran ba su tsaya ga sansanonin soja ba kawai; sun shafi ofisoshin jakadanci, matatun mai, da iskar gas a faɗin yankin, cewar rahoton NDTV.
Babban abin da ya fi girgiza duniya shi ne rufe mashigar ruwan Hormuz da Iran ta yi, wanda ya katse hanyar sufurin makamashi mafi mahimmanci a duniya.
A ƙasar Kuwait, kusan dukkan sansanonin Amurka 13 sun zama kufai, waɗanda ba za a iya sake zama a cikinsu ba sakamakon luguden wuta, abin da ya tilasta wa sojojin gudun hijira zuwa cikin birane.
Sojojin Amurka sun nufi Gabas ta Tsakiya

Kara karanta wannan
Trump zai sauya salon yaki da Iran, sojojin Amurka 2,500 sun nufi Gabas ta Tsakiya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka ta tura karin dubunnan dakarun sojojin ruwa da jiragen yaki zuwa Gabas Ta Tsakiya don karfafa yaki da Iran.
Gwamnatin Donald Trump na nazarin tura sojojin kasa zuwa tsibirin Kharg na Iran domin lalata karfin tattalin arzikin kasar da danyen man fetur dinta.
Jirgin yakin USS Bush ne zai maye gurbin USS Ford a yankin Gulf yayin da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakya ya haura mako uku.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
