Ana Zargin Rasha Ta Kusa Kammala Aika Jiragen Yaƙi Marasa Matuƙa ga Iran

Ana Zargin Rasha Ta Kusa Kammala Aika Jiragen Yaƙi Marasa Matuƙa ga Iran

  • A yayin da ake ci gaba da gwabza yakin Gabas ta Tsakiya, rahotanni sun fara zargin cewa Russia tana kai wa Iran dauki
  • Wani rahoto ya yi zargin cewa Shugaban Rasha, Vladimir Putin na shirin aikewa Iran jiragen yaki marasa matuka
  • Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da ba Iran bayanan sirri, yana mai cewa yana da hujjoji

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Russia – Wasu rahotanni daga kasashen yamma sun bayyana cewa Rasha na dab da kammala aikewa Iran kayayyaki amfani daban-daban.

Daga cikin abubuwan da za ta aika har da jiragen yaki marasa matuka, magunguna da abinci, domin taimaka mata a rikicin da take fuskanta da Amurka da Isra’ila.

Ana zargin Rasha na taimaka wa Iran
Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran da Vladimir Putin na Rasha. Hoto: Alexander KAZAKOV/POOL/AFP
Source: Getty Images

Financial Times ta wallafa cewa majiyoyi masu tushe a bangaren leken asiri sun shaida cewa jami’an Rasha da Iran sun fara tattaunawa a asirce kan batun tura jiragen.

Kara karanta wannan

An 'bankado' wani aikin sirri da Rasha ke yi wa kasar Iran a yakinta da Isra'ila

Ana zargin Rasha da taimakon Iran

Jaridar Independent UK ta ruwaito cewa ana shirin aika jiragen yaki kwanaki kadan bayan hare-haren farko da Amurka da Isra’ila suka kai kan Tehran a watan da ya gabata.

Rahoton ya nuna cewa an fara jigilar kayayyakin ne tun farkon watan Maris, 2026 kuma ana sa ran za a kammala kafin karshen watan.

Wannan na zuwa ne a lokacin da dangantaka tsakanin Moscow da Tehran ke kara karfi, sakamakon goyon bayan da Iran ta dade tana bai wa Rasha tun lokacin mamayar Ukraine.

Martanin Rasha ga zargin taimakon Iran

A gefe guda, Kakakin Kremlin, Dmitry Peskov, ya mayar da martani kan zargin, inda ya ce akwai bayanai na ƙarya da yawa da ke yawo.

Sai dai ya jaddada cewa Rasha na ci gaba da tattaunawa da shugabannin Iran, ba tare da tabbatar da batun jigilar jiragen yaki ba.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya dade yana zargin Rasha da taimaka wa Iran ta fuskar bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta yi abin da ba a yi tsammani ba, ta nemi alfarmar Trump kan Iran

Ya bayyana cewa Moscow ta taba kokarin matsa lamba ga Amurka, inda ta yi tayin dakatar da bai wa Iran bayanai idan Washington ta daina taimaka wa Kyiv.

Rasha tana ƙaryata iƙirarin rahoton
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha. Hoto: Gavril Grigoroc
Source: Getty Images

A cewarsa, yana da hujjoji karara da ke nuna cewa Rasha na ci gaba da bai wa Iran irin wannan taimako, duk da cewa bai fitar da cikakken bayani a bainar jama’a ba.

Iran ta dade tana samar wa Rasha jiragen Shahed, wadanda suka zama muhimmin bangare na hare-haren da Moscow ke kai wa Ukraine.

Rahotanni sun nuna cewa ana harba daruruwan irin wadannan jirage a kusan kowace rana, lamarin da ya tilasta Ukraine bunkasa dabarun kare kai daga irin wannan hari.

Isra'ila ta shammaci kasar Iran

A baya, mun wallafa cewa rundunar tsaron Isra'ila (IDF) na ci gaba da yin dauki dai-dai ga manyan jagorori da kwamandojin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

IDF ta sake hallaka wani babban kwamandan sojojin ruwa na rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) yayin da Amurka ke cewa ana ganawa.

Rundunar IDF ta kashe Alizera Tansgiri ne a wani hari da ta kai yayin da yake ganawa da da wasu jami'an sojojin ruwa na Iran, wanda ya shiga jerin manyan ƙasar da aka kashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng