Hari a Iran: Isra’ila, Amurka Sun Burma Matsala, Majalisar Dinkin Duniya Ta Juyo Kansu

Hari a Iran: Isra’ila, Amurka Sun Burma Matsala, Majalisar Dinkin Duniya Ta Juyo Kansu

  • Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da muhawara ta gaggawa kan harin makaranta a Iran da ya kashe yara 168
  • Kasar Iran, China da Cuba ne suka nemi zaman, suna zargin harin ya saba dokokin kasa da kasa da kuma jin ƙai na duniya
  • Rahoto ya nuna kuskuren harba makami na Amurka ne ya haddasa harin makarantar da ke Minab wanda ya jawo maganganu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya ya ji korafin kasar Iran da China da Cuba kan harin Amurka a makaranta.

Kwamitin zai gudanar da wata muhawara ta gaggawa karo na biyu a ranar Juma’a 27 ga watan Maris, 2026 da muke ciki bayan korafe-korafe da aka kai gabansa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ji korafin Iran kan hari a makaranta
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Reza B, Andrew Caballero-Reynolds.
Source: Twitter

Musabbabin muhawar a Majalisar Dinkin Duniya

Za a yi muhawar ne kan harin da aka kai wata makaranta a Iran wanda ya yi sanadin mutuwar yara da dama, kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Abin ya yi yawa,' Fafaroma ya yi wa Trump da Iran wa'azi mai ratsa zuciya

Shugaban kwamitin, Sidharto Reza Suryodipuro, ya sanar da shirin muhawarar wadda za ta mayar da hankali kan kare yara da cibiyoyin ilimi a lokutan yaƙe-yaƙe na duniya.

An bayyana cewa Iran, China da Cuba ne suka buƙaci a gudanar da zaman, inda suka yi nuni da harin da aka kai wata makaranta a birnin Minab a ranar farko ta yaƙi, 28 ga Fabrairu, 2026.

Rahotanni na farko sun nuna cewa wani makami mai linzami na Amurka ya bugi makarantar ne sakamakon kuskure, kamar yadda wani bincike na sojin Amurka ya bayyana.

Kasashe sun yi Allah wadai da harin Amurka a makarantar Iran
Sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Iran ta yi Allah-wadai da hari a makaranta

Jakadiyar Iran, Somayeh Karimdoost, ta bayyana harin a matsayin “babban take dokokin jin ƙai da kuma haƙƙin ɗan Adam na duniya,” tana mai cewa an kashe yara 168 masu shekaru tsakanin bakwai zuwa 12.

Ta ƙara da cewa kasashen da suka nemi zaman suna sa ran majalisar za ta ɗauki matakin gaggawa da ya dace kan lamarin, saboda girman asarar rayuka da aka samu.

Majalisar mai mambobi 47 ta amince ba tare da ƙuri’a ba cewa za a gudanar da wannan muhawara, bayan wani zaman farko da aka yi kan hare-haren Iran a ƙasashen yankin Gulf, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya janye kai mummunan hari Iran, ya fadi dalilan daukar matakin

A zaman da ya gabata, an yi Allah-wadai da hare-haren Iran a ƙasashen makwabta, tare da kiran a biya diyya ga waɗanda suka rasa rayukansu da dukiyar su sakamakon rikicin.

Majalisar Dinkin Duniya ta magantu kan yakin Iran/Isra'ila

Mun ba ku labarin cewa Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya bukaci Amurka, Isra'ila da Iran su tsagaita wuta, su koma teburin tattaunawa.

Guterres ya ce matukar ba a gaggauta magance yakin da ya barke a Gabas ta Tsakiya ba, to zai iya kai wa matakin da zai fi karfin kowa.

Kasar Iran dai ta sha nanata cewa ba ta neman yaki da rikici da kowa, amma za ta dauki duk matakin da ya dace domin kare 'yancinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.