Iran Ta Yi Gargadi ga Amurka kan Tura Sojoji, Ta Fadi Sakamakon da Zai Biyo Baya

Iran Ta Yi Gargadi ga Amurka kan Tura Sojoji, Ta Fadi Sakamakon da Zai Biyo Baya

  • Kasar Iran ta yi martani mai zafi game da shirin Amurka na kara tura dakarun sojoji zuwa yakin Gabas ta Tsakiya da ake gwabza yaki
  • Iran ta gargadi Amurka kan shirinta tana cewa tana sa ido sosai kan dukkan motsin rundunar Washington duba da shirin da kasar ke yi
  • Kakakin majalisa a Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana cewa duk wani kuskure daga Amurka na iya haifar da mummunan sakamako a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta fitar da kakkausar gargadi ga Amurka kan rahotannin tura karin sojoji zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta yi gargadin ne ga Amurka kan shirinta tana gargadin Washington da kada ta gwada juriyarta a wannan lokaci.

Iran ta yi kakkausar gargadi ga Amurka
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Wannan gargadi ya fito ne daga kakakin majalisa, Mohammad Bagher Ghalibaf, wanda ya wallafa sakon gargadin a shafinsa na X a yau Laraba 25 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Trump ya aika wa Iran bukatu 15 na kawo karshen hare haren Amurka da Isra'ila

Ghalibaf ya ce Tehran na sa ido sosai kan dukkan motsin rundunar Amurka, musamman batun karin sojojin da ake turawa yankin.

Shirin tura dakarun Amurka Gabas ta Tsakiya

Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta shirya tura karin dubunnan dakarun sojojin ruwa da jiragen yaki zuwa Gabas Ta Tsakiya domin karfafa yakin da take yi da kasar Iran.

Gwamnatin Trump na nazarin tura sojojin kasa zuwa tsibirin Kharg na Iran domin lalata karfin tattalin arzikin kasar da danyen man fetur dinta.

Jirgin yakin USS Bush ne zai maye gurbin USS Ford a yankin Gulf yayin da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakya ya cika mako uku cif.

Kalaman Ghalibaf sun zo ne yayin da rahotanni ke cewa Amurka na shirin tura sojoji domin karfafa matsayinta a yankin, matakin da ake ganin wani bangare ne na karin shirye-shiryen soja.

Trump ya samu gargadi daga Iran kan tura dakaru
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Gargadin da Iran ta yi wa kasar Amurka

A cikin wata sanarwar da ya fitar, Ghalibaf ya ce duk wani kuskure daga Amurka zai iya haifar da mummunan sakamako mai girma a yankin.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Iran ba, China na shirin yaki da zai zama barazana ga Amurka

Ya kuma soki Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, yana cewa abin da janarori suka lalata, sojoji ba za su iya gyarawa ba kuma za su iya zama wadanda za su sha wahala ba.

Ya kara da cewa irin wadannan matakai na iya kara dagula halin da ake ciki a yankin, musamman yayin da tashin hankali ke ci gaba da karuwa tsakanin kasashe daban-daban a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya yaba da kyautar Iran ga Amurka

A wani labari, an ji cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana gagarumar kyauta da Iran ta ba Amurka da ta shafi mai da gas da mashigar Strait of Hormuz.

Trump ya bayyana cewa bai yarda da kowa ba, amma ya ce abin da Iran ta yi ya nuna suna hulɗa da mutanen da suka dace wanda lamarin ya ce ya yi matukar ba shi mamaki.

Ya ƙara da cewa Amurka na iya samun iko a Hormuz bayan yaƙi, yana mai hasashen cewa rikicin zai ƙare nan ba da jimawa ba kamar yadda wasu ke fata game da yakin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.