Yaƙi da Iran Ya Raba kan Amurkawa, Ana Ganin Trump Ya Fara Wuce Gona da Iri

Yaƙi da Iran Ya Raba kan Amurkawa, Ana Ganin Trump Ya Fara Wuce Gona da Iri

  • Yakin da Amurka ke ci gaba da gwabza wa da Iran bayan ya shigar wa Iran ya fara jawo damuwa a ƙasar
  • Akalla 59% na Amurkawa sun ce matakin sojin Amurka kan Iran ya yi yawa sosai kuma hakan ya fara jawo damuwa sosai
  • Wasu 45% sun bayyana damuwa da tsadar man fetur a watanni masu zuwa, yayin da ake ci gaba da neman daƙile Iran

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA – Wani sabon bincike da cibiyar bincike ta AP-NORC ta gudanar ya nuna cewa mafi yawan Amurkawa na ganin matakin da Amurka ta ɗauka a yaƙin da ake yi da Iran ya wuce gona da iri.

Binciken ya zo ne a daidai lokacin da yaƙin da Amurka da Isra’ila suka fara ya shiga mako na huɗu, lamarin da ke ƙara jawo muhawara a cikin siyasar ƙasar.

Kara karanta wannan

Iran ta ba Trump mamaki, ya fadi abin da ta yi na bazata da ya aminta da ita

Yan Amurka sun fara magana game da yakin Iran
Shugaban Amurka Donald Trump da ke yaki Iran Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

AP News ta wallafa cewa duk da cewa jama’a ba su sauya wa Shugaba Donald Trump ba, ana ganin rikicin na iya zama babban kalubale ga gwamnatinsa ta jam’iyyar Republican.

Yaƙin Iran ya fara tasiri a Amurka

The Times of Israel ta wallafa cewa 59% na waɗanda aka tambaya sun bayyana cewa matakin sojin Amurka a Iran ya yi yawa.

A lokaci guda, Trump na ci gaba da tura ƙarin jiragen ruwa na yaƙi da sojoji zuwa Gabas ta Tsakiya, abin da ke ƙara nuna ƙarfafa matsin lamba.

Sai dai kuma, shugaban bai fito fili ya bayyana matakin da zai ɗauka gaba ba. Duk da barazanar da yake yi, ya kuma nuna yiwuwar komawa tattaunawar diflomasiyya domin kawo ƙarshen rikicin.

A gefe guda, kusan 40% na Amurkawa har yanzu na goyon bayan yadda Trump ke gudanar da mulki, wanda bai sauya ba idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Kara karanta wannan

Pakistan za ta shiga tsakani a yakin Amurka da Isra'ila ke gwabzawa da Iran

Amma mutane da dama na nuna damuwa kan yadda zai yanke hukunci kan amfani da ƙarfin soji a ƙasashen waje, inda mafi yawansu ke adawa da tura sojojin ƙasa kai tsaye.

Kasar Amurka ta shiga damuwa

Binciken ya kuma nuna cewa matsalar tsadar man fetur na ƙara damun jama’a. Kimanin 45% sun ce suna matuƙar damuwa kan yadda za su iya biyan kuɗin man fetur a watanni masu zuwa.

Wasu na ganin ana wuce gona da iri a yaƙin Iran
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Masoud Pezeshkian
Source: Getty Images

Wannan adadi ya karu daga 30% da aka samu a wani bincike da aka yi bayan sake zaɓen Shugaban ƙasa, Donald Trump.

Duk da wannan damuwa, akwai wani bangare da Amurkawa suka amince a kan hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Sai dai kuma, mutane suna kuma ganin muhimmancin dakile tashin farashin mai da gas a cikin gida.

Wannan yanayi na nuna wani kalubale ga Fadar White House, domin cimma manufofin biyu na zama mai wahala a lokaci guda.

Kasar Iran ta gargaɗi Amurka

A baya, mun wallafa cewa kasar Iran ta yi martani mai zafi game da shirin Amurka na kara tura dakarun sojoji zuwa yakin Gabas ta Tsakiya da ake gwabza yaki.

Kara karanta wannan

Switzerland ta rufe ido, ta dakatar da sayar wa Amurka makamai kan yaƙi da Iran

Iran ta gargadi Amurka kan shirinta tana cewa tana sa ido sosai kan dukkanin motsin rundunar Washington duba da shirin da kasar ke yi a dambarwar da ake yi.

Kakakin majalisa a Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana cewa duk wani kuskure daga kasar Amurka na iya haifar da mummunan sakamako a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng