'Abin Ya Yi Yawa,' Fafaroma Ya Yi wa Trump da Iran Wa'azi Mai Ratsa Zuciya

'Abin Ya Yi Yawa,' Fafaroma Ya Yi wa Trump da Iran Wa'azi Mai Ratsa Zuciya

  • Bayan shafe mako uku ana luguden wuta a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila, Fafaroma Leo ya fito ya yi magana ga shugabanni
  • A wani bayani da ya yi, Fafaroman ya bukaci kasashen da suke gwabza yakin su nemi mafita ta hanyar tattaunawa maimakon kai hare-hare
  • Haka kuma, ya bayyana cewa ba zai iya shiru ba a daidai lokacin da bama-bamai ke kara sauka kan al'umma a kasashen da ke yaki da juna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Vatican - Fafaroma Leo ya sake yin kira a ranar Talata da a tsagaita wuta, tare da bukatar hukumomi su nemi zaman lafiya ta hanyar tattaunawa, yana mai gargadin karuwar ƙiyayya, tashin hankali da asarar rayuka.

Jagoran addinin ya yi magana ne yayin da Amurka/Isra'ila ke cigaba da kai hare-hare Tehran, Iran kuma ke cigaba da luguden wuta a Tel Aviv da kasashen Larabawa.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: An yi wa jirgin Isra'ila ruwan wuta bayan tura shi kai hari

Fafaroma Leo a fadar Vatican
Fafaroma Leo da ya nemi a dakatar da yaki a Gabas ta Tsakiya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Nasihar da Fafaroma Leo XVI ya yi

Rahoton da Anadolu Agency ya nuna cewa Fafaroma Leo ya bukaci a ajiye makami a tattauna domin samar da zaman lafiya a duniya.

“Ina sake jaddada kiran tsagaita wuta, a samar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa, ba da makami ba”

Inji shi ga manema labarai a Castel Gandolfo, Italy.

Fafaroman ya gargadi cewa ƙiyayya na ƙaruwa kuma tashin hankali na tsananta, yana mai ƙarawa da cewa sama da mutum miliyan 1 sun rasa wuraren zama, yayin da da dama suka rasa rayukansu.

“Mu na son yin addu’a domin zaman lafiya, amma ina kira ga dukkan hukumomi da su yi aiki da gaskiya ta hanyar tattaunawa domin warware matsaloli,”

Inji shi.

Wani jawabin Fafaroma a baya

A wani jawabi na daban da ya gabatar a ranar Lahadi, Fafaroman ya nuna damuwa sosai kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da sauran wuraren da yaƙe-yaƙe da tashin hankali suka shafa.

Kara karanta wannan

Yayin da Amurka ke ikirarin tattaunawa, Iran ta yi wa Isra'ila illa da makamai masu linzami

“Ba za mu iya yin shiru ba alhali muna ganin wahalar da mutane da dama ke sha a matsayin waɗanda rikice-rikicen nan suka shafa,”

Inji shi.

Ya yi Allah-wadai da wahalhalun da yaƙe-yaƙe ke haifarwa, yana kiran hakan abin kunya ga dukkan bil’adama da ke zaune a fadin duniya.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump na jawabi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka kuma Fafaroman ya bukaci a ci gaba da addu’a domin a kawo ƙarshen faɗan, kuma hanyoyin zaman lafiya su buɗe ta hanyar tattaunawa ta gaskiya da mutunta darajar ɗan Adam.

Ga bidiyon Fafaroma da Al-Jazeera ta wallafa a X:

Iran ta harba makamai Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Isra'ila ta tabbatar da wasu hare-hare masu zafi da ta ce Iran ce ta kai mata kan wasu gine-gine.

Hotuna da bidiyon da aka fitar sun nuna yadda wasu biranen Isra'ila suka ruguje, lamarin da ya sanya jama'a tofa albarkacin bakinsu.

Baya ga ruguza wurare da dama, gwamnatin Isra'la ta sanar da cewa makamai masu linzami da Iran ta harba sun jikkata mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng