Tashin Hankali: Wuta Ta Kama a Kotun Amurka, Shari'a Ta Tsaya Cak
- Rahotanni sun nuna cewa wata mummunar gobara ta tashi a wata kotun Amurka da ke dauke da manyan ofisoshin jami'an gwamnati
- Tashin wutar ya jawo dakatar da zaman kotu tare da fara dogon bincike game da dalilan gobarar domin sanin matakan da za a dauka
- Hakan na zuwa ne bayan gobara ta tashi a wata matatar mai da ke jihar Texas da kuma hadarin jirgin sama a jihar New York duk a Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Wata mummunar gobara da ta lalata ginin kotun Floyd County a Amurka ta tilasta rufe kotuna tare da kawo cikas ga ayyukan gwamnati a duk faɗin yankin.
Jami’ai sun ayyana dokar ta-baci a harkar shari’a bayan gobarar ta tashi a ginin kotun da ke kan West Fifth Avenue, lamarin da ya hana shiga cikin ginin tare da haifar da fargabar tsaro.

Source: Twitter
CBS News ta wallafa cewa an rufe kotun ranar Talata, kuma ana sa ran za a buɗe ta ranar Laraba, sai dai idan an ƙara tsawaita umarnin.
Yadda gobara ta tashi a kotun Amurka
An fara samun rahoton gobarar ne da rana a ranar Litinin, inda aka fitar da dukkan ma’aikatan da ke cikin ginin nan take, kamar yadda jami’an yankin suka bayyana.
Wasu bayanai da hukumomi suka fitar sun tabbatar da cewa ba a samu rahoton jikkata ko rauni ba ga ko mutum daya da ke cikin ginin.
'Yan kashe gobara sun kai dauki
Jami’an kashe gobara sun shafe sa’o’i suna kokarin shawo kan gobarar yayin da hayaki ya bazu a tsakiyar birnin Rome.
A lokacin da ake kokarin kashe wutar, hukumomin tsaro sun rufe hanyoyin da ke kusa yayin da ake gudanar da aikin ceto wadanda ke cikin ginin.
Ga bidiyon gobarar da shafin Rapid Report ya wallafa a X:
Tarihin kotun Amurka da ya yi gobara
Rahoton tashar CNN ya nuna cewa an gina kotun tun a shekarar 1892, kuma ana tsaka da gyare-gyare ne a lokacin da gobarar ta tashi.
A bayanan da jami’an gwamnati suka yi, sun ce ginin, wanda ke dauke da ofisoshin kula da haraji da rijistar abubuwan hawa, ya lalace sosai.
“Mun gode sosai da saurin kai dauki da kuma ƙoƙarin jami’an agajin gaggawa,”
Inji shugabar kwamitin yankin, Rhonda Wallace a cikin wata sanarwa.
A halin yanzu, hukumomin Amurka sun sanar da cewa ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar da kuma duba matakan da za a dauka.

Source: Getty Images
Gobara ta tashi a matatar Amurka
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Amurka ta sanar da cewa an samu mummunar gobara a babbar matatar man Texas.
Jami'an kashe gobara sun sanar da cewa sun kai agaji da gaggawa domin ganin sun samu nasarar kashe wutar a kan lokaci.
Hukumomi sun sanar da cewa an toshe hanyoyi a kusa da matatar domin ba jami'an tsaro cikakkiyar damar aiki yadda ya kamata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

