Kim Jong Un Ya Gargadi Amurka kan Iran, Ya Yi Maganar Makamin Nukiliya

Kim Jong Un Ya Gargadi Amurka kan Iran, Ya Yi Maganar Makamin Nukiliya

  • Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya sake magana kan yakin Iran da Amurka ta hada kai da Isra'ila ta kaddamar a karshen Fabrairun 2026
  • A bangaren mallakar makamai, Kim Jong Un ya bayyana cewa babu gudu ba ja da baya game da hada makamin nukilya da kasar shi ta riga ta yi
  • Ya gargadi Koriya ta Kudu da ke kawance da Amurka, inda ya kira ta da mai adawa da shi, yana mai cewa zai magance duk wata barazana ga kasar shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

North Korea - Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya yi wa duniya karin bayani kan mallakar nukiliya da kasar shi ta yi.

Kim Jong Un ya yi magana ne yayin wani jawabi a majalisar Koriya ta Arewa bayan sake zaben shi ya cigaba da jagorantar kasar.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta yi abin da ba a yi tsammani ba, ta nemi alfarmar Trump kan Iran

Kim Jong Un yayin duba wasu makamai
Kim Jong Un da wasu jami'an Koriya ta Arewa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin Kim Jong Un ga Amurka

Tashar Al-Jazeera ta wallafa bidiyon jawabin da Kim Jong Un ya yi, inda ya gargadi Amurka game da yakin da ta kaddamar a Iran da ya shafi kasashe.

Yayin da yake jawabi a gaban majalisar, shugaban ya zargi Amurka da aikata “ta’addanci” a yakin da take yi da Iran, yana mai gargadin cewa duk wata barazana ga ƙasarsa za a mayar da martani da ba tare da wasa ba.

Maganar mallakar nukiliyar kasar Koriya ta Arewa

Shugaban Koriya ta Arewa ya bayyana cewa ƙasar shi ba za ta taba ajiye matsayin ta na ƙasar da ta mallaki makaman nukiliya ba.

Bayan sake naɗa shi a matsayin shugaba, Jong Un ya bayyana tsarin mallakar nukiliya a matsayin wanda ba zai canza ba, yana mai alƙawarin ƙara ƙoƙari wajen tinkarar abin da ya kira “maƙiyan ƙasar shi”.

“Za mu ci gaba da ƙarfafa matsayin mu na ƙasa mai makaman nukiliya a matsayin hanya da ba za ta canza ba, tare da ƙara ƙaimi wajen yaƙi da maƙiya,”

Kara karanta wannan

A karshe, Trump ya fadi abin da Iran za ta yi masa a samu zaman lafiya

Inji shi a jawabin da ya gabatar a majalisar dokoki a Pyongyang.

Kim Jong Un a rumbun makamai
Shugaba Kim Jong Un a wajen ajiyar makaman Koriya ta Arewa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cikin jawabin da tashar Farance24 ta ruwaito, shugaban ya tabo batutuwa da dama ciki har da makaman nukiliya, manufofin tsaro, tattalin arziki da kuma dangantaka da Koriya da Amurka.

Ya ce:

“Za mu ci gaba da faɗaɗa da inganta ƙarfin nukiliya domin kare kanmu,”

Haka kuma ya ce ƙasar za ta tabbatar da cewa rundunar makaman nukiliyarta tana cikin cikakken shiri domin tinkarar duk wata barazana

Magana kan Koriya ta Kudu

Kim Jong Un ya bayyana Koriya ta Kudi a matsayin “mafi girman 'yar adawa”, yana mai cewa za su ɗauki matakai masu tsauri a kanta.

Ya kuma ƙara da cewa Pyongyang za ta yi martani a kan duk wani abu da ya keta hurumin ƙasarta ba tare da wani jinkiri ko tausayi ba.

Iran tu ruguza birnin Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa Iran ta kaddamar da sababbin hare-hare zuwa kasar Isra'ila, inda ta ruguza manyan gine-gine da jikkata jama'a.

Kara karanta wannan

Makaman Iran sun razana Netanyahu, ya fito a bidiyo yana neman agaji

Wani bidiyo ya nuna yadda manyan gidaje suka rushe, jama'a na gudu domin tsira da rayuwarsu a hare-haren da Iran ke cigaba da kaiwa.

'Yan Najeriya da dama sun yi martani, suna nuna cewa birnin Tel Avid ya yi kama da yadda Isra'ila ta mayar da Gaza saboda hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng