Iran Ta ba Trump Mamaki, Ya Fadi Abin da Ta Yi na Bazata da Ya Aminta da Ita

Iran Ta ba Trump Mamaki, Ya Fadi Abin da Ta Yi na Bazata da Ya Aminta da Ita

  • Shugaba Donald Trump ya bayyana gagarumar kyauta da Iran ta ba Amurka da ta shafi mai da gas da mashigar Strait of Hormuz
  • Trump ya bayyana cewa bai yarda da kowa ba, amma ya ce abin da Iran ta yi ya nuna suna hulɗa da mutanen da suka dace
  • Ya ƙara da cewa Amurka na iya samun iko a Hormuz bayan yaƙi, yana mai hasashen cewa rikicin zai ƙare nan ba da jimawa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington, DC - US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana game da yakin da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya bayyana cewa Iran ta ba ƙasarsa wata “kyauta” mai matuƙar daraja da ta shafi harkokin mai da iskar gas, da kuma mashigar Strait of Hormuz.

Kara karanta wannan

Hormuz: Iran ta maida martani kai tsaye ga kawayen Amurka bayan barazanar Trump

Trump ya ji dadin kyautar da Iran ta yi wa Amurka
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump, Iran Military Media.
Source: Facebook

Iran ta ba Trump mamaki da abin alheri

Trump ya faɗi haka ne yayin da yake magana da manema labarai a Ofishin Oval, inda aka tambaye shi dalilin da ya sa yake amincewa da Iran, cewar Reuters.

Shugaba Trump ya ce shi ba ya yarda da kowa, kafin ya bayyana cewa:

“Sun yi wani abu jiya da ya ba mu mamaki, sun ba mu kyauta... wacce ta iso yau.”
“Kyauta ce mai girma ƙwarai wadda ta kai darajar kuɗi mai yawa. Ba zan faɗa muku abin da take ba, amma babbar nasara ce.”

Ya jaddada cewa Iran ce kaɗai za ta iya yin irin wannan abu inda ya bayyana jin dadinsa game da lamarin.

Trump ya magantu kan kawo karshen yakin Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Trump ya magantu kan kyautar kasar Iran

Trump ya bayyana cewa kyautar ba ta da alaƙa da batun makaman nukiliya, sai dai tana da nasaba da mai da gas.

Lokacin da aka tambaye shi ko tana da alaƙa da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, sai ya amsa da “Eh.”

Kara karanta wannan

Iran: Trump zai ja baya daga yaki, ya ce sojojin Amurka za su koma gida

Dangane da yiwuwar Amurka ta mallaki mashigar bayan yaƙin, Trump ya ce za mu iya samun iko kan duk abin da muke so.

Ya kuma bayyana cewa yana ganin za a kawo ƙarshen yaƙin nan ba da jimawa ba bayan shafe kusan wata guda ana yaki, cewar France 24.

A wani ɓangare na jawabinsa, Trump ya yi barkwanci cewa lokacin da ya faɗa wa ministan tsaronsa da shugaban sojoji cewa yaƙin Iran zai kusa ƙarewa, sun nuna rashin jin daɗi domin suna son a ci gaba da yaƙi.

Trump ya magantu kan yiwuwar samun zaman lafiya

An ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana abin da ya ke bukata daga kasar Iran domin samun zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu.

Trump ya yi magana ne yayin da aka shiga mako na uku ana gwabza yaki da Iran bayan jerin hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai.

Masu sharhi sun bayyana cewa ba lallai Iran ta saurari bukatar Trump ba lura da cewa ta shafi shirin ta na mallakar makamai masu linzami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.