Ba a Gama da Iran ba, China na Shirin Yaki da zai Zama Barazana ga Amurka

Ba a Gama da Iran ba, China na Shirin Yaki da zai Zama Barazana ga Amurka

  • Wani bincike ya nuna cewa kasar China ta fara wani shiri ta cikin ruwa da masana suka ce yana nuna alamun shirin nuna karfin soja da yaki
  • Rahoto ya ce ayyukan da dakarun sojojin China ke yi sun shafi manyan ruwan duniya da suka hada da tekun India, Pacific da sauransu
  • Hakan na zuwa bayan shafe sama da kwana 20 ana gwabza yaki a Gabas ta Tsakiya tun bayan hare-haren da Amurka/Isra'ila suka kai Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China - Kasar China na gudanar da wani babban aiki na taswira da sa ido a karkashin teku a tekunan Pacific, Indian da Arctic, inda take tara cikakkun bayanai.

Masana harkar soja na cewa lamarin yana da matukar muhimmanci wajen gudanar da yakin jiragen ruwa na karkashin teku da Amurka da kawayenta.

Kara karanta wannan

Amurka ta gano ba za ta iya rusa Iran nan kusa ba, ta fadawa Isra'ila gaskiya

Wani jirgin China a cikin teku
Yadda jirgin ruwan China ke tafiya a ruwa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shirin yaki da kasar China ke yi

Reuters ta wallafa cewa jirgin bincike mai suna Fang Hong 3, mallakin Jami’ar Ocean da ke China, ya shafe shekarun 2024 da 2025 yana zirga-zirga a yankunan tekun kusa da Taiwan, wani sansanin Amurka a Guam da tekun india.

A watan Oktoba 2024, jirgin ya duba wasu na’urorin gano abubuwa a karkashin teku kusa da Japan, sannan ya sake komawa yankin a watan Mayun shekarar.

A watan Maris 2025 kuma, ya rika yawo tsakanin Sri Lanka da Indonesia, musamman kusa da mashigar Malacca wanda yake da matukar muhimmanci ga zirga-zirgar jiragen ruwa.

Masana harkar yaki da jami’an rundunar Amurka sun ce irin bayanai da ya ke tarawa na taimaka wa China wajen fahimtar yanayin karkashin teku domin amfani da jiragen ruwanta na karkashin ruwa da kuma bibiyar abokan gaba.

Times of India ta wallafa cewa akalla jirage 42 sun shafe sama da shekaru biyar suna gudanar da irin wannan aiki a tekunan Pacific, Indian da Arctic.

Kara karanta wannan

Da gaske jiragen Iran sun farmaki ayarin motocin Trump? an samu gaskiyar zance

Bayanin masana kan shirin China

Duk da cewa ana amfani da wannan bincike wajen ayyukan farar hula kamar kamun kifi da neman ma’adanai, masana guda tara sun ce yana da muhimmiyar manufa ta soja.

Wani tsohon shugaban rundunar jiragen karkashin teku ta Australia, Peter Scott, ya ce irin wadannan bayanai na da matukar amfani wajen shirya fagen yaki.

Binciken ya kuma nuna cewa China ta mayar da hankali kan yankunan da ke da muhimmanci ga soja kamar kusa da Philippines, Guam, Hawaii da kuma tsibirin Wake inda Amurka ke da sansanonin soja.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump na wani bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai ma’aikatun tsaro, harkokin waje da albarkatun kasa ta China ba su mayar da martani kan wannan batu ba, haka kuma ma’aikatar yakin Amurka ba ta yi tsokaci ba.

Jirgin Colombia ya yi hadari

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin kasar Colombia ta sanar da cewa wani jirginta dauke da mutane sama da 100 ya yi hadari jim kadan bayan ya tashi.

Kara karanta wannan

Iran ta bude hanya, sojoji Denmarka za su gwabza fada da dakarun Amurka

Ministan tsaron kasar ya sanar da cewa mutane 64 sun rasu wasu da suka jikkata kuma an mika su asibitoci domin samun kulawa.

Shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro ya nuna damuwa game da hadarin, inda ya ce bai kamata haka ta faru da dakarun kasar shi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng