Ana Yakin Iran, Jirgi Dauke da Sojoji Sama da 100 Ya Fado Ya Kama da Wuta

Ana Yakin Iran, Jirgi Dauke da Sojoji Sama da 100 Ya Fado Ya Kama da Wuta

  • Wani jirgin soja dauke da mutane sama da 100 ya yi hadari a kasar Colombia, lamarin da ya jawo mutuwar dakaru da jikkata wasu
  • Ministan tsaron kasar, Pedro Sánchez ya yi magana bayan hadarin, inda ya ce har yanzu ana bincike domin gano sababin faduwar jirgin
  • Yayin da wadanda suka jikkata ke cigaba da samun kulawa, shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro ya fito ya yi magana ga 'yan kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Colombia - A kalla mutane 64 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan jirgin sojoji ya fadi a Kudancin kasar Colombia.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan yankin da jirgin sojojin ya fado, Jhon Gabriel Molina ya tabbatar da faruwar hadarin.

Yadda jirgin Colombia ya yi hadari
Jirgin Colombia da ya kama da wuta. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar CNN ta tattaro bayanin da ministan tsaron Colombia, Pedro Sánchez ya yi game da halin da wasu da suka tsallake rijiya ta baya suka yi.

Kara karanta wannan

An fadi jihar da za a jigbe jiragen yakin Amurka a Arewacin Najeriya

Yadda jirgin soja ya fado kasa

Jirgin samfurin C-130 Hercules ya tarwatse bayan ya fado kasa tare da kamawa da wuta a kusa da garin Puerto Leguízamo da ke yankin Putumayo, kusa da iyakar Peru.

Daga cikin fasinjoji 114 da ke cikin jirgin, akwai sojojin Colombia 112 da kuma ‘yan sanda biyu, sannan akwai ma’aikatan jirgin guda 11.

Bayanin ministan tsaron kasar

Ministan tsaro, Pedro Sánchez, ya ce har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba, yana mai karawa da cewa babu wata alama da ke nuna cewa wasu kungiyoyin masu laifi ne suka kai hari.

Rahoto AP ya nuna cewa Pedro Sánchez ya kuma bayyana cewa jirgin yana cikin yanayin lafiya yayin da ya tashi, kuma ma’aikatan jirgin sun kware a aikinsu.

Wuta ta tashi bayan jirgin ya fadi

Wani bidiyo ya nuna jirgin yana tashi daga filin jirgin Caucaya kafin ya wuce wani yankin karkara, sannan ya fadi bayan dan lokaci kadan, inda aka kiyasta hatsarin ya faru kasa da mil biyu daga filin jirgin.

Kara karanta wannan

Makaman Iran sun razana Netanyahu, ya fito a bidiyo yana neman agaji

Rahotonnni sun bayyana cewa hotuna daga wurin hatsarin sun nuna harshen wuta da hayaki baki mai yawa suna tashi daga tarkacen jirgin.

Jirgin Colombia da ya yi hadari
Yadda ake ceto mutane daga hadarin jirgin Colombia. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wani mai aikin ceto daga yankin, Nicolas Ordoñez, ya ce an kai wasu daga cikin wadanda suka tsira asibitin yankin, yayin da aka kai wasu sojoji da suka jikkata zuwa babban birnin Bogotá domin samun kulawa.

Shugaban Colombia ya magantu

Shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro, ya nuna takaici inda ya ce bai kamata hadarin ya faru ba, yana mai bayyana damuwa kan rashin sabunta kayan aikin sojoji, wanda ya danganta da matsalolin tsarin gwamnati.

Wani rahoto ya nuna cewa jirgin da ya fado rundunar sojin Amurka ce ta ba rundunar sojin saman Colombia shi a shekarar 2020.

Jirgi ya yi hadari a kasar Amurka

A wani labarin, kun ji hukumomin kasar Amurka sun tabbatar da wani hadarin jirgin saman Canada da ya faru a ranar Litinin da ta wuce.

Bayanan da rundunar 'yan sandan birnin New York ta fitar ya nuna cewa jirgin ya yi karo da mota ne yayin da ya zo sauka a Amurka.

Hukumar kashe gobara ta kai daukin gaggawa yayin da jami'an da ke lura da tashi da saukar jirage suka ce an dakatar da aiki a filin jirgin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng