Donald Trump Ya Janye Kai Mummunan Hari Iran, Ya Fadi Dalilan Daukar Matakin

Donald Trump Ya Janye Kai Mummunan Hari Iran, Ya Fadi Dalilan Daukar Matakin

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ba sojojin kasarsa umarnin dakatar da kai hare-hare kan matatun mai da wutar lantarkin Iran
  • A cewar Donald Trump, dakatarwar ta tsawon kwanaki biyar ce kacal, yayin da ya ce Amurka na kan teburin tattaunawa da Iran a yanzu haka
  • Wannan sanarwa ta kawo sauki ga fargabar karancin makamashi a duniya, biyo bayan rufe mashigar ruwan Hormuz da Iran ta yi a kwanakin baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa ya umarci dakarun sojojin Amurka da su dakatar da shirin kai munanan hare-hare kan matatun wutar lantarki da na makamashin Iran.

A ranar Litinin, 23 ga watan Maris, 2026 ne Trump ya ba dakarun sojojin Amurkan wannan umarni, kuma ya ce dakatarwar ta tsawon kwanaki biyar ce kawai.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Iran ta yi martani kan ikirarin Trump na fara tattaunawa kan yakin da ake yi

Trump ya janye kudurin kai hari kan cibiyoyin makamashi da na lantarkin Iran.
Shugaba Donald Trump da hayaki yana tashi a birnin Tehran bayan wani harin Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya janye kai mummunan hari Iran

Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social da manyan baƙaƙe cewa:

"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Amurka da kasar Iran, a cikin 'yan kwanakin nan, sun shiga tattaunawa mai muhimmanci, game da kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
"La'akari da yanayin tattaunawar, da kuma nasarar da ake samu, za a ci gaba da yin irinta a tsawon makon nan (daga Litinin zuwa Alhamis) don ganin ko za a iya cimma matsaya."

Trump ya ƙara da cewa ya umarci ma'aikatar yaƙi da ta dakatar da kowane irin hari na soji, muddin tattaunawar tana tafiya yadda ya kamata.

"Na umarci ma'aikatar kula da harkokin yaki ta Amurka da ta dakatar da dukkan wasu hare-haren soja a kan makamashi da wutar lantarkin Iran na tsawon kwanaki biyar.
"Wannan zai ba da damar tattaunawa da kuma ganin cewa an kammala tattaunawar cikin nasara."

Kara karanta wannan

Yakin Amurka, Isra'ila da Iran ya taba Najeriya, farashin litar fetur ya haura N1350

- Shugaba Donald Trump.

Tasirin wannan sassauci na Trump

Wannan sanarwa ta zo ne a matsayin babban sassauci ga yankin Gabas Ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya. Tun bayan ɓallewar yaƙin, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi, wanda ya haifar da matsalar makamashi a duniya.

Ko a ranar Asabar, Trump ya ba Iran wa'adin sa'o'i 48 ta buɗe mashigar ruwan Hormuz, inda ya yi barazanar "shafe" matatun makamashin ƙasar idan ba ta bi umarnin ba.

Mashigin na Hormuz shi ne hanyar da kashi ɗaya bisa biyar na man fetur ɗin duniya ke bi, wanda barazanar Trump ta kara jawo farashin danyen mai ya haura har zuwa kusan $119.

Shugaba Donald Trump ya ce suna kan tattaunawa da Iran don kawo karshen yakin
Shugaban Amurka, Donald Trump lokacin da ya dura filin jirgin Palm Beach da ke Florida a ranar 27 ga Fabrairu, 2026. Hoto: Mandel NGAN / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Manazarta sun hango zuwan ƙarshen yaƙin

Wakilin jaridar Aljazeera, Osama bin Javaid, ya bayyana cewa wannan sanarwa wata dama ce ga Trump na fita daga yaƙin da ya ƙaddamar ba tare da goyon bayan majalisar Amurka ba.

Kara karanta wannan

Trump ya gaji da jira, ya ba Iran wa'adin awa 48 ko ya yi mata illa mai muni

Shi kuwa masanin harkokin siyasa Mohammed el-Masry, ya nuna damuwa kan abin da zai iya faruwa idan Isra'ila ta yanke shawarar ci gaba da yaƙin ba tare da goyon bayan Amurka ba.

Daga birnin Tehran, dan jarida, Mohamed Vall ya bayyana cewa akwai yuwuwar Iran ta amince da wannan tayi na Trump duk da cewa ta shafe mako uku tana yakin ba tare da gajiyawa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com