Za a Fafata: Kasashe 22 Za Su Tunkari Iran kan Bude Mashigar Hormuz
- Kungiyar kasashen NATO ta yi magana kan kokarin bude mashigar Hormuz da Iran ta toshe saboda hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata
- Hakan na zuwa ne bayan toshe mashigar ya jawo tashin farashin makamashi a fadin duniya, lamarin da ya kara tsadar rayuwa a kasashe daban-daban
- A makon da ya wuce shugaban Amurka, Donald Trump ya caccaki kasashen NATO, ya kira su da matsorata saboda kin goya masa baya a kan kasar Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban kungiyar tsaron kawance ta NATO, Mark Rutte, ya bayyana a ranar Lahadi cewa kasashen kungiyar tare da wasu kawayenta za su taimaka wajen bude mashigar Hormuz.
Mark Rutte ya lissafa Koriya ta Kudu da Japan a matsayin kasashen da za su hada kai da NATO a shirin daukar matakin hadin gwiwa domin dawo da zirga-zirgar jirage a mashigar.

Source: Getty Images
Rahoton Korea Herald bai bayyana ko kasashen NATO za su yi amfani da karfi ne ko kuma hanyoyin diflomasiyya wajen tunkarar Iran ba.
Kasashen da za su tunkari Iran
A wata hira da ya yi, Rutte ya ce kasashe 22 sun hada kai tun ranar Alhamis da ta wuce domin tunkarar aikin bude mashigar Hormuz.
Ya bayyana cewa yawancin su mambobin NATO ne, amma akwai kuma kasashe kamar Koriya ta Kudu, Japan, Australia, New Zealand, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Bahrain da ba su NATO.
Rutte ya yi magana yana mai cewa sun hadu ne domin aiwatar da bukatar shugaba Donald Trump na ganin an bude mashigar Hormuz.
Shugaban ya ce:
“Muna tantance abin da ya kamata, lokacin da ake bukata da yadda za mu aiwatar da shi tare.”
Wasu rahotanni sun nuna cewa Rutte ya kara da cewa da zarar lokaci ya yi, za su dauki matakin da ya kamata su dauka.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Tinubu ya tsallake rijiya, an gano wani mugun shiri da sojoji suka yi na kwace Aso Rock
Karin bayani daga NATO kan Hormuz
A wata hira dabam, Rutte ya ce kasashen da ke cikin shirin na kokarin amsa tambayoyi uku masu muhimmanci:
“Me muke bukata? Yaushe muke bukata? Kuma a ina muke bukata?”
Kalaman nasa na nuna cewa NATO na ci gaba da musayar ra’ayi da kasashe kamar Koriya ta Kudu, Japan da kuma abokan hulda a Turai da Gabas ta Tsakiya, sakamakon kiran da Amurka ta yi na daukar mataki.

Source: Getty Images
A makon da ya gabata, Trump ya soki yadda NATO ta mayar da martani kan Iran, yana mai cewa kungiyar ba za ta iya komai ba idan ba tare da Amurka ba.
Ga bidiyon hirar da aka yi da Rutte da Reuters ta wallafa a X:
Donald Trump ya kafawa Iran sharuda
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka ya bukaci gwamnatin Iran ta cika wasu sharuda domin samun zaman lafiya a tsakaninsu.
Donald Trump ya bukaci Iran da ta daina kera makamai masu linzami na tsawon shekara 5 a cikin sharuda 6 da ya gindaya mata.
Bugu da kari, Trump ya nemi Iran ta daina taimakawa kungiyoyin da ke aiki a Gabas ta Tsakiya kamar Hamas da ke Gaza da Hizbullah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
