Yayin da ake Yaki da Iran, Jirgin Sama Ya Yi Hadari a Kasar Amurka

Yayin da ake Yaki da Iran, Jirgin Sama Ya Yi Hadari a Kasar Amurka

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu hadarin jirgin sama a wani filin sauka da tashin jirage a birnin New York na Amurka
  • Rundunar 'yan sanda ta yi karin bayani game da hadarin yayin da hukumomi suka bayyana cewa an takaita zirga-zirga a wajen
  • Hakan na zuwa ne yayin da yakin Amurka da Iran ke cigaba da daukar hankali a Gabas ta Tsakiya ba tare da alamar kawo karshensa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Rahotanni sun bayyana cewa rundunar 'yan sandan birnin New York na kasar Amurka ta tabbatar da cewa wani jirgin sama ya yi hadari.

Labarin hadarin jirgin saman ya fito ne da safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Maris 2026 kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

Kara karanta wannan

Da gaske jiragen Iran sun farmaki ayarin motocin Trump? an samu gaskiyar zance

Wajen da jirgin Canada ya yi hadari
Jirgin Canada da ya yi hadari a New York. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da tashar Al-Jazeera ta fitar ya fadi yadda jirgin ya yi hadari da matakan gaggawa da jami'an tsaro suka dauka a wajen.

Yadda jirgi ya yi hadari a Amurka

Wani jirgin Air Canada Express mai lamba 8646 daga Montreal ya bugi wata mota a filin jirgi yayin sauka a LaGuardia na New York, lamarin da ya sa aka rufe filin jirgin.

‘Yan sandan New York sun shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa jirgin Air Canada ya yi karo da wata motar hukumar tashoshin jiragen ruwa.

Haka kuma, hukumar kashe gobara ta ce ta kai dauki bayan samun rahoton hatsarin da ya shafi jirgi da mota a kan hanyar saukar jirage.

Karin bayani kan hadari a Amurka

Rahotanni daga wasu majiyoyi sun nuna cewa jirgin nau’in CRJ-900 ya bugi motar ne a yammacin ranar Lahadi. Kamfanin Jazz Aviation, wanda ke aiki tare da Air Canada, ne ke tafiyar da jirgin.

Kara karanta wannan

Iran ta bude hanya, sojoji Denmarka za su gwabza fada da dakarun Amurka

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka (FAA) ta bayar da umarnin dakatar da dukkan tashin jirage zuwa LaGuardia sakamakon hadarin, inda aka rufe filin jirgin har zuwa karfe 05:30 na yamma.

Sanarwar FAA ta bayyana cewa rufe filin jirgin ya faru ne saboda wani yanayi na gaggawa, kuma akwai yiwuwar a tsawaita shi, ba tare da bayar da karin bayani ba.

Yadda jirgin Canada ya yi hadari a Amurka
Jirgin Canada da ya yi hadari a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matsalar da jirgin ya samu

Bidiyoyin da ba a tabbatar da su ba da suka yadu a kafafen sada zumunta sun nuna lalacewar gaban jirgin, inda aka ga ya dan tashi sama. Sai dai kamfanin Reuters ya ce bai iya tabbatar da sahihancin bidiyon ba.

Wani rahoto ya nuna cewa an karkatar da jirage masu sauka zuwa wasu filayen jirage wasu kuma aka mayar da su inda suka taso.

Hukumar kula da harkokin gaggawa ta New York ta gargadi jama’a da su sa ran jinkiri, rufe hanyoyi, da cunkoso, tare da yawan jami’an agaji a yankin Queens da filin jirgin yake.

Bakin jirage sun sauka a Amurka

A wani labarin, kun ji cewa hukumomin Amurka sun tabbatar da saukar wasu bakin jiragen yaki marasa matuka da ba a san daga ina suke ba.

Kara karanta wannan

Gobara ta tilasta wa jirgin yakin Amurka gudu wa daga yakin Iran

Rahotanni sun nuna cewa jiragen sun yi shawagi ne a wani sansanin soji da ministocin Shugaba Donald Trump ke zaune a Washington.

Lamarin ya dauki hankali ne matuka kasancewar ya faru a daidai lokacin da Amurka ta hada kai da Isra'ila tana yaki da kasar Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng