Amurka Ta Gano ba za Ta Iya Rusa Iran nan Kusa ba, Ta Fadawa Isra'ila Gaskiya
- Gwamnatin Amurka ta fito karara ta fadawa Isra'ila cewa yakin da ake da Iran ba abu ne da zai zo karshe nan kusa kamar yadda aka yi zato ba
- Rahotanni sun nuna cewa yakin na cigaba da daukar sabon salo ne ganin yadda Iran ta toshe mashigar Hormuz da harba manyan makamai
- Tun farkon fara yakin, Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi hasashen ba za su wuce mako uku zuwa hudu ba suna gwabwaza da kasar Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Amurka ta sanar da kasar Isra’ila cewa yaki da Iran na iya daukar lokaci fiye da yadda aka fara tsammani a kwanakin baya.
Hakan na zuwa ne yayin da rahotanni suka ce yunkurin bude mashigar ruwan Hormuz da Iran ta toshe zai iya daukar karin makonni da dama.

Source: UGC
Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa Amurka ta yi magana ne yayin da aka shiga mako na uku da fara yakin ba tare da hango alamar karshensa ba.
Me yasa yakin Iran/Amurka zai dade?
Rahoton ya ce burin Washington bai tsaya kan bude mashigar Hormuz kadai ba, har ma da rage tasirin Iran a kan farashin makamashi a duniya baki daya.
A kan haka aka samu rahoton da ke cewa jami’an Amurka na cewa suna son samun sauyi na dabaru ko da kuwa hakan zai dauki lokaci.
A baya ma dai kakakin rundunar sojin Isra’ila, Effie Defrin, ya ce hare-haren kan Iran da kungiyar Hezbollah ta Lebanon za su ci gaba na wasu makonni masu zuwa.
Wani rahoto ya nuna cewa jami’ai a Washington da kawayenta na shirye-shiryen yiwuwar tsawaita shigar Amurka yakin har zuwa watan Satumba, 2026 ko da kuwa rikicin ya ragu zuwa mataki mai sauki.
Asasar rayuka da aka yi a yakin
Hare-haren hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran sun fara ne a ranar 28 ga Fabrairun 2026, inda rahotanni suka ce sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 1,300, ciki har da tsohon Jagoran Tehran, Ayatollah Ali Khamenei.
A matsayin martani, Iran ta kai hare-hare da jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami kan Isra’ila, Jordan, Iraki da kasashen yankin Gulf da ke dauke da sansanonin sojin Amurka.
Maganar Donald Trump a baya
A farkon yakin, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an tsara shirin yakin da Iran ya dauki mako hudu zuwa biyar, amma ya kara da cewa rundunar sojin Amurka na da karfin da zai iya tsawaita yakin fiye da haka.

Source: Getty Images
Al-Jazeera rahoto cewa da yake jawabi daga Fadar White House, Trump ya kare matakin shiga yaki da Iran tare da Isra’ila, yana mai cewa Iran na barazana mai tsanani ga Amurka.
Jita-jitar mutuwar Netanyahu na karuwa
A wani labarin mun kawo muku cewa jama'a da dama a kafafen sada zumunta na cigaba da yada dade radin mutuwar Benjamin Netanyahu.
A cigaba da yada rade-radin ne tun bayan da Firaministan Isra'ila ya fito a wani bidiyo da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sadarwa.
Masu sharhi a kafafen sadarwa kamar Tiktok da X na cigaba da fashin baki game da bidiyon Netanyahu yayin da rade-radin ke karuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


