Makamin da Iran Ta Harba Ya Keta Tsaron Isra'ila, Ya Fada kusa da Cibiyar Nukiliya

Makamin da Iran Ta Harba Ya Keta Tsaron Isra'ila, Ya Fada kusa da Cibiyar Nukiliya

  • Iran ta kai hari kusa da cibiyar nukiliyar Isra'ila dake Dimona, inda gomman mutane ciki har da yara suka jikkata bayan rugujewar gine-gine
  • Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan ababen more rayuwa a Tehran, yayin da yakin Gabas ta Tsakiya ya shiga mako na hudu
  • A gefe guda, harin da Iran ta kai sansanin Diego Garcia ya nuna cewa kasar tana da makamai masu linzami da ke cin dogon zango a wannan yaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila - A daren jiya Asabar, Iran ta harba makaman linzami kan garuruwan Dimona da Arad, kusa da babbar cibiyar nukiliyar Isra'ila.

Harin ya ruguza gine-gine tare da jikkata mutane bakwai sosai, sa’o’i kadan bayan da aka kai hari kan babbar matatar nukiliyar Iran.

Makaman da Iran ta harba sun yi barna a Isra'ila.
Jami'an tsaro da na ba da agajin gaggawa a wurin da makamin Iran ya fada a garin Arad, kasar Isra'ila. Hoto: Ilia YEFIMOVICH / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Makaman Iran sun sauka garuruwan Isra'ila

Kara karanta wannan

Trump ya gaji da jira, ya ba Iran wa'adin awa 48 ko ya yi mata illa mai muni

Jaridar The Times of Israel ta bayyana cewa, wannan ne karon farko da Iran ta kai farmaki kusa da cibiyar binciken nukiliyar Isra'ila tun farkon yakin.

Daga cikin wadanda suka ji rauni sosai a kudancin kasar, akwai wani yaro dan shekara 12 a birnin Dimona da kuma wata yarinya yar shekara 5 a garin Arad, wadanda baraguzan makami suka fada masu.

Wannan luguden wuta ya biyo bayan hare-haren da Iran ta kaddamar akai-akai kan yankin Dimona a ranar Asabar, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Rundunar sojin Isra'ila ta amince cewa ta kasa kakkabe makaman da suka fada biranen Dimona da Arad, wadanda su ne garuruwa mafi girma dake kusa da wannan cibiyar nukiliyar a hamadar Negev.

Martanin Isra'ila da karin hare-haren Iran

Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya tura karin jami'an agaji zuwa wuraren da aka farmaka yayin da Shugaban dakarun kasar ma ya jaddada cewa har yanzu yakin bai kusa karewa ba.

Bayan wadannan hare-hare, Netanyahu da babban kwamandan sojin kasar sun lashi takobin ci gaba da yaki a kowane fanni tun bayan barkewar rikicin da Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Kara karanta wannan

Iran ta ƙaddamar da harin makami mai linzami kan cibiyar haɗa nukiliyar Isra'ila

A wani bangaren kuma, Iran ta farmaki sansanin sojin Amurka da Burtaniya na Diego Garcia dake can tsakiyar tekun Indiya, mai nisan kusan kilomita 4,000, in ji rahoton Bloomberg.

Wannan harin ya nuna cewa ko dai Iran tana da makamai masu cin dogon zango fiye da yadda ake tsammani, ko kuma ta yi amfani da fasahar tauraron dan adam wajen kaddamar da harin ta wata dabarar.

Iran ta farmaki Dimona, garin da ke kusa da cibiyar nukiliyar Isra'ila
Rumbun makamin nukiliyar Isra'ila da ke Dimona, Kudancin saharar Negev. Hoto: THOMAS COEX/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin yakin Isra'ila/Amurka da Iran

Ita dai Amurka da Isra'ila sun bayar da dalilai daban-daban na yin wannan yakin; wasu lokuta su ce suna so ne su tursasa mutanen Iran su yi bore su kifar da gwamnati, ko kuma su lalata makaman nukiliya da na linzami na kasar.

To amma har yanzu babu alamar boren ya faru, sannan katse hanyoyin intanet ya sa yana da wuya a san ainihin abin dake faruwa a cikin Iran.

Tuni dai tasirin wannan yakin ya mamaye duniya, inda ya janyo tashin farashin abinci da man fetur.

Trump ya tura karin sojoji Gabas ta Tsakiya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Amurka ta tura karin dubunnan dakarun sojojin ruwa da jiragen yaki zuwa Gabas Ta Tsakiya domin karfafa yakin da take yi da kasar Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Gwamnatin Shugaba Donald Trump na nazarin tura sojojin kasa zuwa tsibirin Kharg na Iran domin lalata karfin tattalin arzikin kasar da danyen man fetur dinta.

Jirgin yakin USS Bush ne zai maye gurbin USS Ford a yankin Gulf yayin da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakya ya cika mako uku cif.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com