Babbar Magana: Putin Ya Aika Sako ga Mutanen Iran ana tsaka da Yaki da Amurka

Babbar Magana: Putin Ya Aika Sako ga Mutanen Iran ana tsaka da Yaki da Amurka

  • Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya tuna da al'ummar Iran yayin da ake ci gaba da yaki a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Vladimir Putin ya taya al'ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran murnar ganin zuwan sabuwar shekara ta Nowruz
  • Shugaban na Rasha ya kuma aiko sako gare su kan yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan kasarsu

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Moscow, Rasha - Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya taya al'ummwr Iran murnar sabuwar shekara ta Nowruz.

Vladimir Putin ya bayyana cewa Rasha aminiya ce kuma abokiyar haɗin gwiwa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Putin ya taya mutanen Iran murna
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin Hoto: Sergey Fadelchev
Source: Getty Images

Tashar Press tv ta kasar Iran ta bayyana cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar a ranar Asabar, 21 ga watan Maris 2026.

Me Putin ya gayawa al'ummar Iran?

Kara karanta wannan

An zo wajen: Trump ya yi magana kan tsagaita wuta a yakin Amurka, Isra'ila da Iran

Fadar Kremlin ta bayyana cewa Putin ya aika da wannan saƙon ne ga jagoran addini na Iran, Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei, jaridar The Economic Times ta kawo labarin.

A cewar saƙon, Putin ya tabbatar wa shugabannin Iran da al’ummar ƙasar cewa Rasha za ta ci gaba da kasancewa aminiyar Iran kuma abokiyar haɗin gwiwa a waɗannan lokuta masu wahala, kuma yana fatan a samu nasarar shawo kan yaƙin Amurka da Isra'ila.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Vladimir Putin ya yi wa al'ummar Iran fatan shawo kan waɗannan jarrabawowin masu tsanani cikin mutunci, sannan ya jaddada cewa a wannan lokaci mai wahala, Moscow za ta ci gaba da kasancewa abokiyar kwarai kuma amintacciyar abokiyar haɗin gwiwa ga Tehran."

Rasha ta yi Allah wadai da hare-hare

Rasha ta bayyana cewa hare-haren Amurka da Isra'ila a kan Iran sun jefa daukacin Gabas ta Tsakiya cikin rikici, sannan sun haddasa babban rikicin makamashi a duniya.

Sai dai, ana muhawara kan girman goyon bayan da Moscow ke ba wa Iran a halin yanzu.

Wasu majiyoyin Iran sun bayyana cewa sun samu ƙarancin taimako na zahiri daga Moscow a cikin wannan babban rikici da Iran ke fuskanta tun bayan kifar da gwamnatin Shah da Amurka ke goyon baya a juyin juya halin 1979.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana shirin da ta yi a kan Trump

A cikin wani saƙo na ranar 9 ga watan Fabrairu, Putin ya taya Ayatollah Khamenei murnar zaɓarsa a matsayin sabon jagoran addini na Iran.

Tun farkon fara zaluncin Isra'ila da Amurka a kan Iran a ƙarshen watan Fabrairu, Rasha ta ci gaba da yin Allah-wadai da ayyukan Washington da Tel Aviv, tana mai bayar da tayin taimakawa wajen rage rikice-rikicen yankin.

Putin ya taya al'ummar Iran murnar shigar sabuwar shekara
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka da Isra'ila suna yaki da Iran

Amurka da Isra'ila sun fara sabon zagaye na hare-hare a kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026, kimanin watanni takwas bayan sun ƙaddamar da hare-hare a kan ƙasar.

Nan take Iran ta fara mayar da martani ta hanyar harba gungun makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a kan yankunan da Isra'ila ta mamaye da kuma sansanonin sojojin Amurka da kadarorinsu a ƙasashen yankin.

Rasha ta gayyaci jakadan Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rasha ta fusata bayan wani hari da Isra'ila ta kai a kasar Lebanon da ya jawo mutane da dama suka samu raunuka.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta gayyaci jakadan Isra’ila Oded Joseph kan harin da aka kai wa ‘yan jaridar tashar RT a Lebanon.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta bayyana harin a matsayin wanda aka nufa kai tsaye kan fararen hula.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng