Ana cikin Yaki da Amurka, Isra'ila, Shugaban Iran Ya Samo Mafita ga Kasashen Musulmi

Ana cikin Yaki da Amurka, Isra'ila, Shugaban Iran Ya Samo Mafita ga Kasashen Musulmi

  • Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi tsokaci kan dangantakar da ke tsakanin kasarsa da kasashen Musulmi
  • Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa akwai makiyan da ke kokarin lalata dangantakar da ke tsakanin kasashen Musulmi
  • Shugaban na Iran ya kuma nuna cewa kasarsa ba ta taba neman kera makaman nukiliya ba domin hakan ya sabawa addini

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi magana kan samar da tsaro a yankin Yammacin Asiya.

Pezeshkian ya yi kira da a samar da tsarin tsaro na Musulunci wanda zai maye gurbin kasancewar baƙi a Yammacin Asiya tare da kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a yankin.

Shugaban Iran ya ba kasashen Musulmai shawara
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce ya yi waɗannan kalaman ne a cikin wani saƙon bidiyo a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Ali Larijani: Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ya dauki zafi, ya tura sako ga Amurka da Isra'ila

Me shugaban Iran ya ce kan kasashen Musulmi?

Ya aika sakon ne a lokacin bikin sabuwar shekara da kuma ƙaramar Sallah (Eid al-Fitr), wadda ke nuna ƙarshen watan Ramadan mai albarka.

"Ba mu da niyyar samun saɓani da ƙasashen Musulmi; ba ma neman rikici ko yaƙi da ƙasashen Musulunci. Su 'yan uwanmu ne."

- Masoud Pezeshkian

Tashar Aljazeera ta ce Pezeshkian ya kuma ƙara da cewa wani maƙiyi "maci amana", ta hanyar ayyukansa, shi ne ke bayan takaddamar da ta faru a tsakanin Musulmi.

Shin Iran na neman kera makaman nukiliya?

"Ba mu taɓa neman makaman nukiliya ba. Duk lokacin da muka haɗu da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci [Sayyed Ali Khamenei] tare da mambobin Majalisar Tsaro da kwamandoji, ya kan bayyana cewa makaman nukiliya haramun ne a addinance."
"Babu wani jami'i a Jamhuriyar Musulunci da zai iya matsawa zuwa ga kera makaman nukiliya na karkashin ƙasa ko kuma karkata tsarin zuwa wannan hanyar."

Kara karanta wannan

China ta gaza hakuri, ta sake yunkurowa kan yakin Amurka da kasar Musulunci ta Iran

"Duk da haka, Amurka da shugabanta sun yaudari duniya su yarda cewa muna da niyyar matsawa zuwa ga makaman nukiliya don haddasa kisan kiyashi."
"Abin takaici, kafofin yaɗa labarai na duniya suna karɓar waɗannan ƙaryar kuma suna ba da rahotanni bisa kansu."

- Masoud Pezeshkian

Shugaban Iran ya ba kasashen Musulmi shawara
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wace mafita ya samo ga kasashen Musulmi?

Ya kara da cewa mafita don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Asiya ita ce ƙasashen Musulmi na yankin su kafa tsarin tsaro don tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali a yankin.

"Ba mu buƙatar kasancewar baƙi a yankin; ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Musulunci, za mu iya kafa 'majalisar Musulunci ta Gabas ta Tsakiya' tare da tsara dangantakarmu ta tsaro, tattalin arziki, al'adu, da siyasa a cikin wannan tsarin."

Iran ta kaddamar da sababbin hare-hare

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta kasar Iran ta kaddamar da sababbin hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

IRGC ta sanar da gudanar da rukuni na 70 na harin ramuwar gayya da take ci gaba da kaiwa mai suna Operation True Promise 4.

Rundunar IRGC ta ce wannan sabon farmakin ya nufi wurare sama da 55 da Amurka da gwamnatin Isra'ila suka mamaye a faɗin yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng