Ana cikin Murnar Sallah, Iran Ta Shammaci Amurka da Isra'ila a Sababbin Hare Hare

Ana cikin Murnar Sallah, Iran Ta Shammaci Amurka da Isra'ila a Sababbin Hare Hare

  • Rundunar IRGC ta kasar Iran ta nuna cewa a shirye ta ke domin ci gaba da fafatawa da Amurka da Isra'ila
  • IRGC ta kaddamar da sabon farmaki wanda ya tunkari birane da dama a Isra'ila tare da sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya
  • Rundunar ta bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka wajen kai hare-haren

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da gudanar da rukuni na 70 na harin ramuwar gayya da take ci gaba da kaiwa mai suna Operation True Promise 4.

Rundunar IRGC ta ce wannan sabon farmakin ya nufi wurare sama da 55 da Amurka da gwamnatin Isra'ila suka mamaye a faɗin yankin.

Iran ta kai hare-hare kan Amurka da Isra'ila
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar IRGC ta fitar ranar Asabar, 21 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban rashi a ranar Sallah, kakakin rundunar IRGC ya mutu a harin Isra'ila

Iran ta farmaki Amurka da Isra'ila

IRGC ta bayyana farkon sa'o'in wannan sabon harin da cewa sun kasance "fashe-fashe masu ƙarfi, barkewar wuta, da kuma gungun hayaki" a duk faɗin yankunan da aka nufa.

Ta ce lokacin da aka kai hare-haren, wato a jajiberin ranar ƙaramar Sallah (Eid al-Fitr) wadda ke nuna ƙarshen watan alfarma na azumin Ramadan, yana nuna sabon yanayi ga Musulmi.

A cewar sanarwar, an nufi sansanonin sojojin Amurka guda biyar a lokacin wannan samame, waɗanda suka haɗa da al-Kharj a Saudi Arabia, al-Dhafra a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Ali al-Salem a Kuwait, Erbil a yankin Kurdistan na Iraƙi, da kuma babban ofishin runduna ta biyar ta sojojin ruwan Amurka da ke Bahrain.

Wadanne makamai aka yi amfani da su?

Rundunar ta ce an kai hare-haren ne ta hanyar amfani da tsarin makamai masu linzami na Qiam da Emad tare da jirage marasa matuƙa, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta kira ruwa, Iran ta kaddamar da sababbin hare hare masu zafi

Ta bayyana wannan mataki na ramuwar gayya a matsayin wani ɓangare na babban tsari na "raunana maƙiyi a hankali".

Iran ta harba makamai kan Amurka da Isra'ila
Makami mai linzami na Iran da aka harba Hoto: @IRIran_Military
Source: Twitter

Wuraren da aka farmaka

Sanarwar ta ƙara da cewa, ayyukan da IRGC ta gudanar sun mayar da hankali ne kan yankuna masu muhimmanci a tashar jirgin ruwa ta Haifa da kuma birnin Tel Aviv.

Daga cikin sauran wuraren da aka aka ambata an farmaka akwai Hadera, Kiryat Ono, Savion, da Ben Ami.

Ta ce an harba makami mai linzami na Khorramshahr-4 da kuma makaman Qadr masu ɗauke da bama-bamai da dama, waɗanda suka yi barna "fiye da yadda maƙiyi yake zato," kuma suka taimaka wajen daɗa taɓarɓarewar yanayi a yankunan da aka mamaye.

Trump ya magantu kan tsagaita wuta da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya tabo batun tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da Iran.

Shugaba Donald Trump ya yi watsi da batun tsagaita wuta da Iran, a yakin da ake gwabzawa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta shiga uku, Iran ta kaddamar da sabon makamai mai hatsari

Trump ya bayyana cewa zai iya tattaunawa da Iran amma ba batun tsagaita wuta, saboda Amurka ta kusa yin nasara a kanta.

.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng