Iran: Trump zai Ja Baya daga Yaki, Ya Ce Sojojin Amurka za Su Koma Gida

Iran: Trump zai Ja Baya daga Yaki, Ya Ce Sojojin Amurka za Su Koma Gida

  • Shugaban Amura, Donald Trump ya nuna alamar a da baya a yakin da ya hada kai da Isra'ila ya kaddamar a Iran a karshen watan Fabrairun 2026
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Donald Trump ke cigaba da nuna ya samu nasara a kan Iran tare da cewa ya gama lalata makamansu
  • A nata bangaren, Iran ta yi martani game da furucin Donald Trump, inda ta caccake shi tare da nuna shakku kan cewa zai janye dakarunsa a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaba Donald Trump ya tayar da kura yayin da ya ce yana nazarin yanje wasu sojoji a Gabas ta Tsakiya ana tsaka da yaki da Iran.

Trump ya bayyana haka ne a daren Juma'a, 20 ga Maris 2026 yayin da yakin da ya kaddamar a Iran ya cika mako na uku ba tare da kawo karshensa ba.

Kara karanta wannan

Kasashe 5 da suka kira Iran ta waya, suka nuna ana tare bayan fara yaki da Amurka

Shugaba Donald Trump da sojojin Amurka
Donald Trump na yi wa sojojin Amurka jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Fadar White House ta wallafa bayanin da Donald Trump ya yi shafinta na Facebook, inda shugaban ya yi ikirarin cewa yana samun nasara kan Iran.

Trump zai ja da baya a yakin Iran

A wata sanarwa da ya fitar, shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka na nazarin rage ayyukan sojinta a Gabas ta Tsakiya.

“Muna daf da cimma manufofinmu, muna nazarin rage manyan ayyukan sojinmu a Gabas ta Tsakiya dangane da Iran,”

Inji shugaba Trump, yana lissafa wasu manufofi ciki har da rage karfin makamai masu linzami na Iran da kuma kawar da rundunar saman da ta ruwa ta kasar.

Ya kara da cewa:

“Dole ne a kula da mashigar Hormuz tare da sa ido daga sauran kasashen da ke amfani da shi — Amurka ba ta amfani da shi!
"Idan akwai bukata, za mu taimaka wa wadannan kasashe, amma bai kamata hakan ya zama dole ba idan an kawar da barazanar Iran."

Kara karanta wannan

Trump ya yi magana kan amfani da makamin nukiliya a yaki da Iran

Martanin Iran ga Donald Trump

Wani babban jami’i daga Tehran ya shaida wa CNN cewa Iran ba ta yarda da ikirarin Trump cewa Amurka na nazarin rage ayyukan sojinta ba.

“Sabanin ikirarin Trump na rage ayyukan soja a yankin, Iran ba ta da irin wannan fahimta kuma ta gano cewa matsayin sojin abokan gaba a yankin bai sauya sosai ba,”

- Inji jami’in

Jami’in Iran ya yi watsi da kalaman shugaban, yana mai cewa wata dabara ce da Trump ke yi domin kulla makirci, bayan rikice-rikicen da suka biyo bayan rufe mashigar Hormuz.

Yadda hanyar mashigar Hormuz ta ke
Mashigar Hormuz da Iran ta hana wasu kasashe wucewa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Farashin mai ya kara tashi a ranar Juma’a zuwa Dala 112 kan kowace ganga, yayin da mashigar Hormuz da ke samar da kusan kashi 20 cikin 100 na man duniya ke ci gaba da kasancewa a rufe a wasu lokutan.

An hango bakon jirgi a Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wasu jami'an gwamnatin Amurka sun bayyana cewa sun hango wani bakon jirgin yaki maras matuki a Washington.

Kara karanta wannan

Bayan Trump ya nuna damuwa, Faransa ta kira Iran kan tsayar da hare hare

An hango jirgin yakin da ba a san daga ina ya fito ba a saman wani sansanin soji da manyan ministocin Donald Trump ke zama.

Lamarin ya jawo tambayoyi game da tsaron Amurka, musamman lura da yakin da kasar ke cigaba da yi da Iran a Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng