Iran Ta Gano Makircin Amurka a Yakin da Ake Yi domin Haɗa Ta Fada da Makwabta

Iran Ta Gano Makircin Amurka a Yakin da Ake Yi domin Haɗa Ta Fada da Makwabta

  • Jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya yi magana game da yaki da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya
  • Khamenei ya ce hare-haren da aka kai Turkiyya da Oman ba su da alaka da sojojin Iran ko kawayenta, yana mai musanta hannu kai tsaye
  • Ya bayyana hare-haren a matsayin “aikin makirci” da makiyan Iran suka shirya domin haddasa rikici tsakanin ƙasashe makwabta, tare da tayar da fitina

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Jagoran addinin Musulunci a Jamhuriyar Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya magantu kan ci gaba da yaki da Isra'ila.

Khamenei ya bayyana damuwa kan makircin da ake kullawa Iran a yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta zargi ana neman hada da fada ta makwabtaka
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Reza B, Andrew Caballero-Reynolds.
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da Al Jazeera ta samu, jagoran Iran ya bayyana cewa hare-haren baya-bayan nan na shirin makirci ne da rashin adalci.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta jawo wa kanta, Rasha ta shiga kafar wando daya da ita kan hari a Lebanon

Yadda yakin Iran da Isra'ila ya barke

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila wacce ke samun goyon bayan Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.

Yakin akalla ya kwashe mako uku kenan tun bayan harin farko a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaro.

Khamenei ya soki makircin wasu ƙasashe a yakin da ake yi
Sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Ana zargin kai hari da sunan Iran

Khamenei ya na magana ne kan hare-haren da aka kai Turkiyya da Oman da cewa ba su da alaka da sojojin Iran.

Ya jaddada cewa ba rundunar sojin Iran ba ce ko kawayenta suka aiwatar da wadannan hare-hare, yana mai ƙaryata zarge-zargen da ake yadawa.

Ya kara da cewa wadannan hare-hare “aikin makirci ne” da makiyan Iran suka shirya domin haddasa rikici tsakanin ƙasashe makwabta.

A cewarsa, manufar hakan ita ce tayar da fitina da rashin jituwa tsakanin kasashen yankin domin cimma wata manufa ta siyasa.

Kara karanta wannan

Yadda Isra'ila ta amsa bukatar Trump, Netanyahu ya magantu kan kawo karshen yaki

Gargadin da Khamenei ya yi kan lamarin

Khamenei ya kuma gargadi cewa irin wadannan abubuwa na iya faruwa a wasu kasashe, yana mai kira ga kasashe su yi taka-tsantsan, cewar Turkiye Today.

Ya bukaci shugabanni da jama’a da su guji fadawa cikin rudani ko yaudara da irin wadannan dabaru na makiya ke amfani da su domin sake hada su fada da makwabta da ba su da matsala da su.

Isra'ila ta zargi Iran da mata kutse

Mun ba ku labarin cewa Isra’ila ta zargi Iran da kutsawa cikin kyamarorin tsaro da dama domin leƙen asiri tun bayan barkewar yakin Gabas ta Tsakiya.

Kamfanin tsaron yanar gizo na ya ce masu kutse sun yi amfani da kyamarori domin tattara bayanai kan wuraren hari wanda ya ce ya yi mata illa sosai.

Rahoto ya ce Isra’ila ma ta taba yin kutse a kyamarorin zirga-zirga a Tehran kafin harin da ya kashe Ali Khamenei a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.