Isra'ila Ta Jawo wa kanta, Rasha Ta Shiga Kafar Wando Daya da Ita kan Hari a Lebanon

Isra'ila Ta Jawo wa kanta, Rasha Ta Shiga Kafar Wando Daya da Ita kan Hari a Lebanon

  • Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta gayyaci jakadan Isra’ila Oded Joseph domin karin bayani kan harin da aka kai
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa Isra'ila ta kai wani hari ya jikkata ‘yan jaridar RT a kasar Lebanon a yakin da ake yi
  • Jakadan Isra’ila ya ki yin tsokaci ga manema labarai kafin ganawa a Moscow, yana mai cewa baya son makara yayin da ake jiran bayani

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Moscow, Russia - Kasar Rasha ta fusata game da wani hari da Isra'ila ta kai a Lebanon wanda ya jawo jikkata mutane da dama.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta gayyaci jakadan Isra’ila Oded Joseph kan harin da aka kai wa ‘yan jaridar tashar RT a Lebanon.

Rasha ta gayyaci jakadan Isra'ila bayan wani hari
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha. Hoto: Gavril Grigoroc.
Source: Getty Images

Rahoton Al Jazeera ya tabbatar da cewa harin ya faru ne a ranar Alhamis 19 ga watan Maris din shekarar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Yadda Isra'ila ta amsa bukatar Trump, Netanyahu ya magantu kan kawo karshen yaki

Rasha ta musanta zargin taimakawa Iran

Wannan takaddama na zuwa ne yayin da Isra'ila da Amurka ke zargin Rasha da taimakawa Iran ta wasu hanyoyi a yakin da ake yi.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa kasar Rasha ta yi martani game da zarginta da ake yi da ba da bayanan sirrin sojojin Amurka.

Maganar ta fito ne bayan tattaunawar waya tsakanin Shugaba Donald Trump da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin.

Rahoto ya zargi Moscow da bai wa Tehran bayanan wuraren jiragen ruwan yaki da jiragen sama na Sojojin Amurka a yankin.

Rasha ta soki Isra'ila kan hari kan 'ya'yanta
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Abir Sultaan.
Source: Getty Images

Harin Isra'ila ya jikkata yan Rasha

Lokacin da manema labarai suka tare shi kafin shiga ginin ma’aikatar a Moscow, jakadan ya ki amsa tambayoyi, yana cewa baya son makara.

A ranar Alhamis, wasu ‘yan tawagar RT da ke kan aiki a kudancin Lebanon sun samu raunuka sakamakon harin sama da Isra’ila ta kai.

Dan jarida Steve Sweeney da mai daukar hoto Ali Rida Sbeity sun jikkata, kuma Rasha ta ce za ta sanar da jakadan matsayarta.

Kara karanta wannan

Iran ta yi luguden wuta yayin da Larabawa ke tsaka da taro a Saudiyya

Rasha ta fusata bayan harin Isra'ila

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta bayyana harin a matsayin wanda aka nufa kai tsaye kan fararen hula.

Ta jaddada cewa ‘yan jaridar sun sanya rigunan kariya masu alamar “press”, suna dauke da kyamarori da makirufo a lokacin harin.

Ta kuma kara da cewa an kai harin ne a yankin da babu cibiyoyin soja, abin da ya sabawa dokokin jin kai na kasa da kasa, cewar rahoton Asia Pacific.

Larijani: Rasha ta yi Wa Iran ta'aziyya

Mun ba ku labarin cewa kisan da Isra'ila ta yi wa babban jagoran tsaron kasar Musulunci ta Iran, Ali Larijani ya fara jawo hankalin shugabannin kasashen duniya.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya nuna alhini tare da aika sakon ta'aziyya ga jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei kan wannan babban rashi.

Shugaba Putin ya bayyana Larijani a matsayin “abokin kwarai,” na Rasha, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kawance kasar da Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.