Yadda Isra’ila Ta Amsa Bukatar Trump, Netanyahu Ya Magantu kan Kawo Karshen Yaki
- Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan tsoma Amurka cikin yakin da suke yi da Iran
- Netanyhau ya ce Isra’ila ta kai hari kan Iran ita kaɗai, ya ce yaƙin zai ƙare da wuri fiye da yadda ake tsammani
- Ya musanta cewa Isra’ila ce ta jawo Amurka cikin yaƙin, yana mai cewa zargin hakan ba shi da tushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi karin haske kan ci gaba da yakin da kasarsa ke yi da Iran.
Netanyahu ya bayyana cewa ƙasarsa ce kaɗai ta kai harin da aka kai kan filin gas na Pars na Kudanci a Iran a makon nan.

Source: UGC
Netanyahu ya ce Isra’ila za ta dakatar da duk wani ƙarin hari kan babban filin iskar gas na Iran bisa buƙatar shugaban Amurka Donald Trump, cewar Al Jazeera.
Yakin Iran/Isra'ila ya shiga makonni
Yakin da ake ci gaba da yi tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka ya shafe kusan mako uku kenan ana yi.
Hare-haren daga kowane bangare ya yi sanadiyyar rasa rayukan al'umma da manyan jami'an gwamnati da fararen hula.
A harin farko da aka kai kan Iran, jagoran addini a kasar, Ali Khamenei ya rasa ransa da wasu daga cikin manyan jam'ian tsaro.

Source: Getty Images
Netanyahu ya magantu kan kawo karshen yaki
Firayim ministan ya bayyana cewa yaƙin Iran zai iya ƙarewa cikin gaggawa fiye da yadda mutane ke tsammani.
Haka kuma ya jaddada cewa duk wani yunkuri na Iran na rufe mashigan ruwan Hormuz ba zai yi nasara ba.
A yayin taron manema labarai da aka watsa kai tsaye, Netanyahu ya kuma musanta zargin cewa gwamnatinsa ce ta jawo Amurka shiga yaƙin Iran, yana mai cewa wannan magana ba gaskiya ba ce.
Ya ce:
"Iran na ƙoƙarin tilasta wa duniya ta hanyar rufe wata muhimmiyar hanya ta sufurin ruwa ta duniya, wato mashigan Hormuz. Wannan ba zai yi aiki ba.”

Kara karanta wannan
Trump ya yi magana da babban jigo a tsaron Amurka ya yi murabus saboda yaki da Iran
“Wannan zargin cewa mu ne muka ja Amurka cikin lamarin ba wai ƙarya kawai ba ce, abin dariya ne.”
Ya ƙara da cewa tun fiye da shekara guda da ta gabata, Trump ya gaya masa cewa dole ne a tabbatar Iran ba ta mallaki makaman nukiliya ba, cewar Reuters.
Netanyahu ya ce Trump na bin duniya bashin godiya saboda jagorancin da yake yi wajen kare makomar duniya, yana mai yabawa rawar da ya taka a wannan rikici.
Iran ta yi wa Amurka lalata a yaki
Mun ba ku labarin cewa rundunar kare dakarun juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi ikirarin yi wa Amurka barna a yakin da ake yi.
IRGC ta yi ikirarin cewa ta kai farmaki kan jirgin saman yaki na Amurka lokacin da yake shawagi a sararin samaniyar Iran.
Mahukunta a Amurka sun tabbatar da cewa jirgin ya samu matsala lokacin da yake gudanar da aiki a Iran wanda ya kwashe kusan mako ana yi.
Asali: Legit.ng
