Kasar Musulunci Ta Iran Ta Sabawa Saudiyya da Najeriya, Ta Sanar da Ranar Karamar Sallah
- Kasar Musulunci ta Iran ta ayyana ranar Asabar, 21 ga watan Maris, 2026 a matsayin ranar Karamar Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan
- Hukumomin Iran sun sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a yau Alhamis, 29 ga watan Ramadan, dom haka za a cika azumi 30 gobe Juma'a
- Haka zalika, kasar Iraki ta bi sahun makwafciyarta, ta sanarda ranar Asabar mai zuwa a matsayin ranar idin karamar Sallah
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Hukumomin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sanar da cewa musulmin kasar za su cika azumi 30 a gobe Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026.
Iran ta sanar da cewa ranar Juma’a ce za ta kasance ranar karshe ta watan Ramadan a kasar, yayin da za a fara bikin karamar Sallah (Eid al-Fitr) a washe gari ranar Asabar.

Kara karanta wannan
Bayan sanarwar Saudiyya, Sarkin Musulmi ya fadi ranar da za a yi karamar Sallah a Najeriya

Source: Getty Images
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwar da ta fito daga ofishin jagoran addinin kasar, Mojtaba Khamenei, da yammacin yau Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa bayan duban jinjirin wata da aka yi a ranar 29 ga Ramadan, an tabbatar da cewa Juma’a ita ce rana ta 30 ga watan Ramadan mai albarka.
"Gobe Juma'a, za ta kasance rana ta 30 ga watan Ramadan mai albarka, sannan kuma za a yi Eid al-Fitr watau karamar Sallah washe gari, wanda ke nuna ƙarshen lokacin azumi," in ji sanarwar.
Kasar Iraki ta bi sahun Iran
Haka kuma, kasar Iraki wacce mafi yawan al’ummarta ‘yan Shi’a ne, ta bi sahun wannan sanarwa ta Iran, kamar yadda babban malamin Shi’a, Ayatollah Ali al-Sistani ya sanar.
Babban malamin na Iraki ya bayyana cewa sanar da ranar Sallah ta dogara ne da ganin jinjirin watan Shawwal, kamar yadda tsarin kalandar Musulunci ya tanada.
An nada Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran koli na Iran a watan Ramadan, bayan rasuwar mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a hare-haren farkon yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran.
A bana, ranar karshe ta Ramadan ta zo daidai da lokacin bikin Nowruz, wanda ake yi a kasar Iran domin nuna farkon bazara, in ji rahoton Arab News.

Source: Getty Images
Muhimmancin Ramadan ga Musulmi
Azumin Ramadan na daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, inda miliyoyin musulmi a duniya ke azumi daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.
Haka kuma, ana karfafa wa musulmi musamman masu rufin asiri gwiwa domin su taimaka wa talakawa ta hanyar bayar da sadaka domin rage radadin rayuwa ga masu karamin karfi.
Saudiyya ta sanar da ranar Sallah
A wani labarin, kun ji cewa Saudiyya ta tabbatar da cewa ba a samu sahiihin rahoton ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1447AH ba a ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan.
Masarautar Saudiyya ta bayyana cewa musulmi za su cika azumi 30 cif a wannan shekara, tare da ayyana ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026 a matsayin ranar karamar Sallah.
Wannan dai na zuwa ne bayan kammala azumin watan Ramadan, wanda bisa ga wannan sanarwa, zai cika kwanaki 30 a bana.
Asali: Legit.ng
